Kannywood
Kalli hotunan Jaruma Sadiya Kabala Tare Da Sabon Mijinta
Advertisment
Jarumar Finafinan Hausa Sadiya Ahmad Kabala ta sake yin aure.
Wata majiya ta shaida mana cewa a jiya ne aka daura auren jarumar a garin Kaduna. Tun bayan mutuwar auren jarumar a shekarar 2018, Sadiya ba ta dawo a masana’antar Kannywood ba, sai ta bazama wajen kasuwancin sayar da kifi gami da takalman mata da jikkuna domin neman dogaro da kan ta.
Wannan dai shi ne karo na 2 da jarumar ta yi aure a tarihin rayuwar ta.
Mun yi bakin kokarin mu wajen neman karin bayani game da auren nata, amma abin ya ci tura.
Advertisment
Muna yi maki fatan alheri Hajiya Sadiya. Allah yasa gidan ki ne na har abada, amin.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com