Sirrin ‘Ya Mace : Sarkakiyar sanin inzalin mace
Kama daga sanin ainahin wurin da mace ta fi jin dadi a taba mata, da yin inzali fiye da sau daya, sanin ilimin yadda jin dadin jikin mace yake ta fannin jima’i abu ne da a da ya gagari masana kimiyya.
To amma yanzu kamar yadda Linda Geddes ta gano, wasu gwaje-gwaje da aka yi na zurfafa bincike sun fara bayyana abubuwan da ba a gane ba a da.
Ga bayaninta.
A jikin na’urata ta wankin tufafi, akwai wani abin dannawa.
Idan har kana son ka kunna wannan inji ka yi amfani da shi to sai ka danna wannan abu (makunni) zuwa wani dan lokaci, kuma ya kasance ka danna abin daidai yadda ya dace.
Idan ba ka danna da kyau yadda ya kamata ba, na’urar ba za ta tashi ba, kuma idan ka danna wannan abu da karfi, sai na’urar ta yi wani kara.
Amma idan ka lakanci yadda abin yake, mai sauki ne, sai ka ga wata ‘yar fitila ta kama, ya fara aiki, inda za ka ji yana wata kara da kai kasan ya kama aiki yadda ya kamata.
A karshe kawai sai ka fara ganin wankakkun tufafinka suna ta fita ta wani bangare na na’urar bayan wani dan lokaci.
Kayanka sun fita fes, sai dai kawai ka diba ka je ka shanya.
To amma wannan abu fa ga wanda aka koya wa yadda ake amfani da na’urar ne.
Idan ba haka ba sai dai kawai ka yi ta kame-kame kana son amfani da na’urar abu ya gagara.
To bayan wannan, yanzu kuma ka yi tunanin yadda inzalin mace yake.
JD Salinger ya taba rubuta wata kasida da ke cewa, ”jikin mace kamar molo yake sai kwararren mawaki ne zai iya kada shi yadda ya kamata”.
Ka taba shi ko ka shafa shi, yadda ya dace, sai ka kai mace wani zango, da cikin wasu ‘yan dakikoki za ta rasa inda take a duniyar nan.
Amma idan ba ka san yadda za ka yi mata abin da ya dace ba, abin da zai iya biyo baya, sai ciwo da damuwa ko kuma lami kawai.
Wannan ya sha bamban matuka da yadda namiji yake, domin shi gogan, in dai har mazakutarsa za ta tashi, wasan da za a yi mata na ‘yan mintina zai sa ya yi inzali ( ya fitar da mani).
Me ya sa inzali yake da matukar dadi?
Me ya sa mata suke yin inzali fiye da sau daya a lokaci daya?
Kuma, ko da gaske ne ma akwai wannan wurin da ake cewa mace ta fi jin dadi idan an taba mata shi?
Wadan nan na daga tambayoyin da suka dade suna ba wa masana kimiyya wahala wajen sanin amsarsu.
”Mun yi nasarar zuwa duniyar wata amma ba mu fahimci yadda jikinmu yake ba sosai,” inji Emmanuele Jannini na jami’ar birnin Rum, Tor Vergata, wanda ya dauki kusan tsawon shekarunsa na aiki (koyarwa da bincike) domin kokarin ganowa.
A shekarun nan masana ilimin jima’i na sosai sun yi ta bincike da nazari da dama a kai, kuma a karshe dai sun fara ganin haske na fahimtar yadda wasu abubuwan suke.
Kwakwalwa na tafarfasa.
Watakila babban kokarin da za a ce masana kimiyya sun yi shi ne, na shawo kan mata, su kawar da kunya da wasu al’adunsu, su yi wasa da jikinsu domin jin dadi da biyan bukatar jima’i da kansu.
Ko kuma ma su sadu da namiji, a bainar masu binciken kimiyya har ma da na’urar daukar hoton aikin kwakwalwar mutum (fMRI) a wannan lokaci na saduwa.
Daya daga cikin jagororin wannan bincike shi ne Barry Komisaruk, na jami’ar Rutgers da ke New Jersey, wanda yake son ya tabbatar ko bambancin kwakwalwa zai iya sa a fahimci dalilin bambancin jin dadin jima’i tsakanin mace da namiji.
Ta tabbata cewa, duk da bambancin yadda suke ji a lokacin jima’in, kusan aiki iri daya kwakwalwar namiji da ta mace suke yi a lokacin inzali.
Kamanceceniyar namiji da mace a yayin inzali ta fi bambancinsu yawa, nesa ba kusa ba, ” inji Komisaruk.
”Abin da muke gani shi ne, kwakwalwar ce gaba dayanta take kama aiki gadan-gadan.”
Wannan, kila shi zai iya bayyana abin da ya sa inzali ke mamaye jikin mutum gaba daya.
Abu ne kamar a ce, idan daji gaba daya ya kama wuta, da wuya ka ce ga daga inda wutar ta tashi.
”A yayin inzali, idan komai ya kama aiki a lokaci daya, wannan zai kawar da bambancin aikin wani bangare da wani bangare,” Kamar yadda Komisaruk ya yi bayani.
Kila wannan ne ma ya sa ba ka iya tunanin komai a wannan lokacin.
Akwai wuraren da ke da alhakin kula da jin dadi a kwakwalwar mutum, inda a duk lokacin da wani sako ya je wannan wuri, mutum yake jin matukar dadi.
Wannan ne ma ya sa, bera zai iya zabar samun wannan jin dadi a maimakon abinci, wanda har ma zai iya hakuri da abincin yunwa ta kama shi har ya mutu, in dai zai sami wannan jin dadi.
Bayan jima’i, abin da ke jawo jin dadin wannan bangare na kwakwalwa, sai hodar ibilis ta koken (cocaine) da sauransu (ampphetamine da caffeine da nicotine da chocolate).
Ba mamaki ashe mutum ya kan so idan ya yi inzali yake son ya kara yi.
Bayan inzali, akwai wasu muhimman bambance-bambance da ake gani, wadanda za su iya bayyana abin da ya sa yanayin mace da namiji yake bambanta a lokacin.
Komisaruk da Kachina Allen sun gano wata sheda ta farko-farko da ke nuna cewa wasu bangarori na kwakwalwar namiji ba sa jin duk wani wasa da ake yi wa mazakuta ko marenansa, jim kadan bayan ya fitar da maniyyi.
Sabanin haka, ita mace irin wadan nan bangarori na kwakwalwarta suna jin irin wannan wasa idan an yi mata a wurin farjinta, bayan ta samu biyan bukatar farko.
Yadda jin dadi yake;
Idan wannan hoton aikin kwakwalwa ya haifar da cece-kuce, to wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da kokarin fahimtar yadda inzali ya kasu daban-daban.
Shi azzakari yana da jijiya ko hanya daya ce kawai, ta kai wa kwakwalwa sako.
Shi kuwa farjin mace yana da irin wadan nan jijiyoyi ko hanyoyi uku ko hudu.
A mazaunin farjin mace akwai abin da ake kira dan-tsaka (clitoris), wanda yake a bakin farjinta.
Maganar wanda ya gano shi kansa dan-tsakan a tsakanin masana kimiyya, an ce wata abar muhawara ce ita ma.
Domin sai a karni na 16 ne ma aka fara bayyana abin, a matsayin wani wuri ko abu na musamman, wanda kowa ce mace take da shi, wanda kuma taba shi, ke sa mata jin dadi.
A littafin Realdo Columbo, mai suna De re anatomica, wanda aka wallafa a 1559, ya bayyana dan-tsaka a matsayin ”cibiyar jin dadin mace”.
Amma kuma a sauran karnin da suka biyo baya, sai masana kimiyyar jikin dan adam, ba su ba maganar jin dadin mace muhimmanci ba, kuma a kan haka, kusan aka manta ma da maganar dan-tsaka.
A karni na 20 ne maganarsa ta kara tasowa, amma duk da haka masana kimiyya da dama, ba su ba shi muhimmanci ba.
Duk da cewa Sigmund Freud ya yarda cewa mata za su iya samun inzali, amma ya yi amanna cewa inzalin da mace baliga za ta yi sakamakon shiga ko taba cikin farjinta, ya fi wanda za ta yi idan jin dadin ya taso daga dan-tsakanta ne.
A rubutun da ya yi, ya ce idan mace ta kasa ko kuma ba ta samun yin inzali daga jin dadin da ta samu na amfani da cikin farjinta, hakan ya shafi matsalar rashin balaga ce ta jima’i.
Idan haka gaskiya ne, to sai a ce, akwai mata masu yawan gaske da ba su fahimci yadda jin dadin jikinsu yake ba na jima’i.
Kusan kashi 30 da 40 na mata sun ce ba su taba yin inzali ba ta hanyar jima’i (tabarya a cikin turmi) kawai.
Ko da yake da yawa kuma sun ce suna samun biyan bukata (inzali) ta hanyar yi musu wasa da dan-tsakansu (clitoris).
Maganar cewa inzali ta sanadin saduwa da mace ta farjinta shi ne inzalin da ya fi muhimmanci, ko ya fi duk wani inzali, abin ya bata ran masu rajin kishin mata da yawa.
Saboda hakan kamar yan
a nuna cewa matan da ba sa samun irin wannan inzali, kamar ba sa kokarin samun hakan ne sosai.
To dangane da hakan za a iya cewa, ke nan, samun irin wannan nau’in biyan bukata (inzali) na jima’i dama ce ga kowace mata ko kuma sai wasu da suka dace ne kawai?
Shin abu ne ma da zai iya yuwuwa a ce mace ta yi inzali idan ba ta da dan-tsaka?
Barry Komisaruk ya yi sa’ar kama matakan farko na amsa wadan nan tambayoyi, a lokacin da yake nazarin yadda beraye suke jima’i.
Wata rana, a lokacin da yake tura wani dan tsinken karfe a farjin macen bera, sai ya ga ta yi wani abu da ya ba shi mamaki.
”Ina taba kofar yankin da ke tsakanin farjinta da hanyar mahaifarta (cervix) sai kawai ta tsaya kyam (macen beran),” ya ce.
Ba wannan ba kadai, a lokacin irin wannan jin dadi ga alama ba ta jin duk wani ciwo ko radadi.
Bayan wannan ne sai kuma mai binciken ya koma kan mata, da wannan gwaji nasa, kuma ya gano daidai irin abin ya gani a kan macen bera, wato jin dadi a cikin farji yana hana mace jin ciwo.
Amma ta yaya hakan ke faruwa?
Domin gano hakan, Komisaruk ya gudanar da bincike tare da Beverly Whipple, inda suka yi nazari a kan matan da ke fama da raunin laka iri daban-daban.
A binciken, sun gano cewa, su wadan nan mata, duk da cewa hanyar jijiyoyin da ta tashi daga yankin farjinsu zuwa kwakwalwarsu ta toshe, ko ta yanke,(saboda raunin da suka ji), matan suna ji idan an taba farjinsu ko can cikin farjin (cervix).
Wasu daga cikin matan, har sukan fitar da mani (inzali) sakamakon tattaba musu wurin, duk kuwa da cewa hanyar da ke aikawa da sako daga matancin nasu (farji) zuwa kwakwalwa ta yanke.
”Matan da ke fama da rauni a lakarsu, wadanda ba sa jin kamar dan-tsakansu na jikinsu, duk da haka suna yin inzali idan aka tattaba musu farjinsu domin jin dadi,” kamar yadda Komisaruk ya ce.
”Wannan ga alama ita ce babbar shedar da ke tabbatar da cewa mace na yin inzali sakamakon jin dadi a cikin farjinta.”
Dalilin shi ne, daga jijiyoyin da ke kusa da lakarta, sakon jin dadi (na tattaba farjin) yake tafiya zuwa kwakwalwa.
”Mata suna bayyana inzalin da suke yi (na sanadin) idan an tattaba dan-tsakansu a matsayin karamin jin dadi kuma na waje.
Shi kuwa inzalin da suke yi a sanadin samun jin dadi a cikin farjinsu, sukan bayyana shi a matsayin, jin dadi na ciki kuma wanda yake shafar dukkanin jikinsu.
Wannan watakila saboda jijiyoyin da suke kai sako kwakwalwa daga dan-tsaka, daban suke da jijiyoyin da suke kai sako kwakwalwa daga ainahin cikin farjinsu ne,” kamar yadda Komisaruk ya yi bayani.
Kuma game da yadda (abin mamaki) jin dadi a cikin farji yake hana mace jin zafin ciwo, watakila jijiyoyin da suka hadu da laka (spinal cord) su ne suke hana aikawa da wannan sako, na jin ciwo zuwa kwakwalwa.
To idan jijiyoyi daban-daban ne suke kai sakon jin dadi daga wurare daban-daban na matancin mace, kuma dukkanin biyun kowanne zai iya haifar da inzali, to za a iya cewa kenan wasu sassan na cikin farji sun fi wasu sassan haifar da dadi ga mace?
To takamaimai daidai wane wuri kenan mata da miji za su nema a cikin farjin matar, domin samar da wannan jin dadi da zai jawo inzali, wanda ke samuwa a sanadin jin dadi na cikin farji ( wanda yake ratsa jikinta gaba daya)?
Matattara (G spot ): Wannan wuri shi ne matattarar jin dadi wanda masana ke wa lakabi da G spot da harshen Ingilishi.
Da dadewa wannan wuri mai farin jini, shi ne aka sanya a gaba.
A farkon shekarun 1980 ne aka kirkiro masa wannan lakabi (G spot) saboda kwararren likitan matan nan na Jamus, Ernst Grafenberg.
A shekarar 1950 ne likitan ya bayyana wani sashe na gaban farjin mace wanda yake da daidai da wurin da mafitsara take a daya bangaren bangon.
A wasu bincike-binciken da aka yi bayan nasa na farko, an gano tarin jijiyoyin jini da wasu jijiyoyin da kuma baki bakin jijiyoyin da mani ke bi, wadanda dukkaninsu sun tattaru a daidai wannan wuri.
A kan haka ne ake ganin tattaba wannan wuri, ta hanyar jin dadi musamman a wasu kadan daga cikin mata zai iya sa su tsartar (fitarwa da karfi) da wani ruwa dan kadan daga mafitsararsu, wanda kuma ba fitsari ba ne.
Daga gano wannan wuri kuma, sai labari ya fara fita a game da wannan dan wuri mai ban mamaki da ta’ajibi, da ke gaban bangon farjin mace.
Sai ma’abota soyayya (maza da mata) suka rinka dukufa domin gano wurin, kuma abin takaici sau da dama ba sa iya gano shi.
Wasu mata masu rajin kare ‘yancin mata (feminists) sai suka ce, yadda ake yayata muhimmancin wannan wuri (G spot), wata dabara ce kawai ta maza, domin mayar da hankali kan yin jima’i ta hanyar shigar da zakari cikin farjin mace, bayan da hankali ya karkata zuwa ga muhimmancin dan-tsaka (clitoris) a jima’i, a lokacin bunkasar da aka samu ta ilimin jima’i a shekarun 1960 da kuma da 70.
Shedar tabbatarwa ko kuma karyata cewa akwai wannan wuri (G spot) ba ta da inganci ko karfi sosai kuma yawanci ana zuzuta ta ne.
Wani nazari da ya musanta tabbatar wannan wuri, ya dogara ne ga wani hoto na asibiti da aka dauka na wata mace daya kawai.
Rikici kan ainahin sunayen daidai na bangarori ko sassan cikin farjin mace da kuma maganar daga ina wannan halitta ta cikin farjin ta fara kuma ina ta kare ya kara kawar da muhawara kan wurin (matattarar jin dadi).
Amma duk da haka an lura da cewa akwai bambanci na zahiri tsakanin matan da suke cewa suna yin inzali idan suka samu jin dadi a cikin matancinsu (jima’i), da kuma wadanda suka ce ba sa yin inzali ta wannan jin dadin.
A shekarar 2008, Jannini ya wallafa sakamakon wani bincike da ya kunshi mata tara da suke yin inzalin ta hanyar jima’i turmi da tabarya (zakari cikin farji) da kuma wadansu 11, wadanda su kuma, suka ce ba sa yin inzali ta wannan hanya kadai (wato sai an hada da taba wasu wuraren).
Kuma wani bincike da aka yi na asibiti ya gano cewa wadanda suke yin inzalin, suna da kaurin fata a daidai wannan wuri da ake cewa matattarar jin dadin (G spot), yayin da su kuma wadanda ba sa inzalin fatarsu ta wurin ba ta da irin wannan kauri.
Daga nan ne sai Jannini ya yanke cewa wannan bambanci watakila shi ne shedar tabbatar wannan wuri, da ake muhawara a kan kasancewarsa da kuma rashinsa. Amma karin wasu bincike-binciken sun sa a kara tunani a kan lamarin.
”Kalmar wuri na iya sa a ga kamar wani abu ne da za ka danna ko ka tura ka samu inzali ko jin dadi,” ya ce.
Tana nufin akwai wani abu na zahiri da ko dai yana wurin ko kuma ba ya nan. Ba wanda ya iya bayyana wannan abu karara a matsayin wuri.”
To tun da ba wani maballi ba ne, menene kenan? A wurin masu bincike da dama, amsar mai sauki ce: kuma ita ce dan tsaka.
Ko da yake a wurin mutane da yawa dan-tsaka wani abu ne kawai mai kamar siffar kwayar fi (pea) a karkashin saman fatar bakin farji, binciken baya-bayan nan ya nuna cewa abin ya wuce girman yadda aka dauke shi.
Nazari ya nuna abin ya kai tsawon kusan inci uku da rabi ko tsawon dan yatsan hannun yawancin mutane.
Abin ya taho ne daga cikin saman farji har zuwa baki, inda a karshe ya dan fito.
Yawancin mutane suna ce masa dan-tsaka, kuma suna ganin shi ne bangaren da ya fi sa mace jin dadi a jikin wannan dan dogon abu, wanda kafafunsa kuma sun rabu ko sun bude a kofar farjin.
Za kuma a iya bayyana shi da cewa azzakari ne mai kai biyu.
Daman kuma dukkaninsu, wato azzakari da shi dan-tsakan irin jijiyarsu daya.
Kuma sun samo asali ne daga farkon halittar jiki daga wuri daya.
Yayin da na mace yake karewa a matsayin dan-tsaka, shi kuwa na namiji sai ya zama azzakari da marena.
Amma kuma suna da wani bambanci mai muhimmanci, domin shi azzakari ba ya ci gaba da girma da zarar mutum ya balaga kamar yadda kwayar halittar mazancinsa (testosterone) ke samuwa.
Shi kuwa dan-tsaka yana ci gaba da girma inji Jannini, ”ba wai dan karamin azzakari ba ne kawai,”
F
arji ma yana samun sauyi sakamakon kasancewar kwayoyin halittar matanci, wanda wannan zai iya taimakawa wajen fahimtar abin da ya sa sha’awar mace ke sauyawa tsawon rayuwarta.
Wannan sarkakiya za ta iya sa a gane cewa abu ne mai wuyar gaske a tabbatar ko kuma a musanta cewa akwai wurin da ake cewa matattarar jin dadin mace (G spot).
Ba abu ne mai sauki ba, ka sa mace jin dadi daga gaban bangon farjinta kadai.
Yayin jima’in za ta iya kasancewa kana gugar bangaren cikin dan-tsakan da kuma mafitsararta.
Karin binciken da Jannini da Odile Buisson suka yi a Saint Germain da ke Faransa ya tabbatar da hakan.
To sai dai abin yana kara sarkakiya a wajen wasu matan, domin shigar zakari cikin farjinsu zai iya a wannan lokacin ya rika tattaba waje da cikin dan-tsakansu, kuma su ji dadi a sanadin hakan.
Misali a 2009, wata mata mai shekara 42 ta je asibitin Rachel Pauls, wata likitar mata a Cincinnatin Ohio da ke Amurka.
Matar an haife ta ba tare da mafutsara ba, kuma an yi mata tiyata domin gyara mata wasu daga cikin wadannan matsaloli.
Pauls ta ce matar tana yin inzali na ban mamaki. Ta gaya wa likitar cewa tana samun yin inzali akalla sau biyu a duk lokacin da ta yi jima’i.
Daya a lokacin wasa da dan-tsakanta da hannu kuma na biyun a lokacin saduwa da ita kawai.
Wannan labari ya ba wa Pauls sha’awa, saboda mafitsarar matar da kuma wurin da ake cewa matattarar jijiyoyin nan (G spot) duka ba sa wurin da ya kamata a ce suna nan.
Sannan kuma dan-tsakanta shi ma yana daidai bakin saman kofar farjinta ne.
”Bisa ga dukkan alamu wannan shi ya sa take yawan yin wannan inzali mai kyau,” inji Pauls. Wato a duk lokacin da azzakarin zai shiga farjinta sai ya gogi dan-tsakan.
Ko girman dan-tsaka yana da tasiri?
Wannan ya haifar da wani tunanin kuma. Pauls tana tunanin ko girma, da kuma wurin da dan-tsakan mata masu lafiya yake, yana da tasiri kan yadda suke yin inzali cikin sauki a lokacin jima’i (ta cikin farjinsu)?
Saboda haka ne sai likitar da wasu abokan aikinta suka samo wasu mata goma da suka ce ba kasafai suke samun yin inzali ba, ko kuma ma ba sa yi a lokacin jima’i, da kuma wasu matan 20 da suka ce su kuma suna yin inzali kusan ko da yaushe.
Likitocin sun yi amfani da na’ura wajen daukar hoto da bayanin yadda dan-tsakan matan yake a lokacin jima’i.
Daga nan sai suka gano cewa, idan dan-tsakan ba shi da girma kuma yana da nisa daga farjin mace, da wuya wannan mata ta yi inzali ta hanyar shigar zakari ko wani abu cikin farjinta.
Idan aka duba wadan nan nazarce-nazarce za a ga cewa akwai hanyoyi da yawa da mace za ta iya samun inzali.
Ko dai ta hanyar jin dadi a cikin farjinta (shigar azzakari ko wani abu) ko tattaba dan-tsakanta ko kuma yi mata duka biyun a lokaci daya.
Karin nazarin da Komisaruk ya yi ya nuna cewa sakonnin jin dadi daga sassan matancin mace daban-daban hadi da kan nononta, duka suna haduwa a wuri daya, na gaba dayan kwakwalwarta, ko da yake, ya dan bambanta a sassan kwakwalwar.
Komisaruk ya ce, ”akwai abin da yake haddasa kowane irin inzali kuma kowanne da irin dadin da ke jawo shi,”
”Watakila wannan shi ya sa hada jin dadin dan-tsaka da cikin farji da kuma hanyar mahaifa a lokaci daya, yake sa mata jin tsananin dadin inzali ko fitar da mani, wanda ke cike da sarkakiya ko wuyar fahimta, kamar yadda matansuke bayyanawa, cewa abu ne da ba za ka iya ba da misalinsa ba”
Su kuwa matan da ba kasafai suke samun yin inzali ba lokacin jima’i na cikin farjinsu ko kuma duk wani nau’i ma na jima’i, sakon Pauls gare su mai sauki ne, kuma shi ne ‘a jarraba wasu hanyoyin’.
Likitar ta ce, ”sai mata su zo wurina a matsayin marassa lafiya, su ce, ba sa yin inzali, saboda haka lalle suna ganin suna da wata matsala.
Ba wata matsala a jikinsu. Kusan kowa yana da dan bambanci da wani.
Wasu matan suna bukatar samun jin dadi sosai na tsawon lokaci a dan-tsakansu a lokacin jima’i, wasu kuwa sai an dan dage kadan, saboda haka sai mazansu watakila sun yi amfani da hannu ko wani abu.
Abin dai shi ne, mata su sani cewa, idan ba su yi inzali ba lokacin saduwa da su ta farji kai tsaye, wannan ba wata matsala ba ce.”
Dakta Emmanuele A Jannini yana da karin sako ga mata: ”Ba jima’i kadai za ki mora ba, ki mori dadin sanin kanki, da fahimtar wacece ke a yau, domin kila ki zama daban gobe.”
Kuma ka da ki rena tarin hanyoyi daban-daban na samun inzali wadanda ake da su.
”Ka da ki dauki jikin mace kamar na’urar da a ko da yaushe za ta yi abu kamar yadda ta saba,” ya ce.
Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The mystery of female orgasm