Uncategorized

Mutane Biyar Sun Rasa Rayukansu A Wajen Turmutsutsun Karbar Zakkar 500 A Katsina

…jami’an tsaro sun kama wanda ya raba zakkar

Akalla mutane biyar ne suka rasa rayukan su wajen karbar zakkar Naira dari biyar biyar a jihar Katsina.

Wadanda suka rasa rayukan na su sun kunshi kananan yara guda 4 da wata mata mai kimanin shekaru 40.

Lamarin ya faru ne a yayin da darururuwan mutane suka taru a gidan mutumin da ke raba zakkar mai suna Kamal Ma’a Gafai, a yankin Rafin Dadi da ke jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah ya shaidawa manema labarai cewa banda wadanda suka rasu, akalla mutane 15 sun jikkata.

Ya ce an kai mutane 15 din asibiti inda aka yi masu magani aka kuma sallame su.

Shi kuwa Gafai mai raba Zakka, DSP Isah ya ce yanzu haka ya na hannun su kuma sun shiga bincike akan shi.

©Faceboo/Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button