Uncategorized

Da Yardar Allah Buhari Zai Zarce A Zaben 2019, Idan Ya Gama Kuma Ni Zan Maye Gurbinsa A Zaben 2023, Inji Hanarabul Gudaji Kazaure

Da Yardar Allah Buhari Zai Zarce A Zaben 2019, Idan Ya Gama Kuma Ni Zan Maye Gurbinsa A Zaben 2023, Inji Hanarabul Gudaji Kazaure
Dan Majalisa mai wakiltar Kazaure, Roni, ‘Yan Kwashi a Majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Jigawa, Honorobul Muhammadu Gudaji Kazaure a wani hira da aka yi da shi ya bayyana cewar idan Allah ya kai mu a  shekarar 2019 Buhari zai zarce da yardar Allah ko da abokan gaba ba sa so. Sannan ya kara da cewar bayan Buhari ya gama shekarunsa 8 a shekarar 2023 shi zai mikawa mulkin Nijeriya, wannan shine fatanshi.
Dan Majalisar, dukda yadda ya shahara da ba da dariya a dakin majalisar wakilai ta tarayya, a hirar da aka yi da shi ya nuna da gaske yake yi, domin a cewarsa, Nijeriya na bukatar shugaban kasa matashi, shugaban majalisar dattijai da na wakilai duka matasa, bayan Buhari ya gama nashi mulkin.
Masu karatu me za ku ce kan hakan?
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button