Uncategorized

Ban -Saniba Ko Za’a Iya Samun Irin Matata A Wanannan Zamanin…….. ❔


Ya zamo wajibi in baku labarin abinda ya faru tsakanina da matana ya sanya nake tunanin ko za’a samu irinta a wannan Duniyar tamu, 

Bayan munyi aure ba’a jimaba sai aka turani (Course) Germany ala tilas na tafi na barta domin babu hali mu tafi tare da ita kullum muna waya sai da na shafe watanni Hudu curr, 

Alhamdulillah ranar da zamu dawo ana Gobe kusan kwana mukayi muna waya 
Ta tambaye ‘:Dan Allah Meye nafi bukatar tayi min na tarya, nace wallahi ni bani bukatar komi fiye da ita kanta ita nafi bukata kafin komi ni ko abinci bani bukatar tayi min mai yawa ni itace burina kuma kar ta fadi ma Sauran Dangi yanzu na fison sai mun-kammala da ita kafin kowa yasan na dawo gida, tace an gama cikin murna, 

Bayan Allah yayi na iso Gida sai muka kashe Sa’oi masu yawa muna tare sai da ta Gamsar dani 100%, sannan muka ci Abinci bayan mun kammala nitsuwa sai naga tana KUKA 

hankali yayi matikar tashi Sabila da irin yanayin da ta shiga, 
Sai nace me kuma ya faruwa? 

sai tace kasan Mahsifiyata tana Asibiti!! kamar yadda na sheda maka tun Shekaran jiya, 
yau kwanaki uku kenan, to lokacin da kayi waya ka iso cikin Kaduna lafiya wallahi lokacin kuma aka kirani a Gida aka sanar dani cewa Ummata ta Rasu,!! 

naji tsoron kar na fada maka lokacin da ka shigo in katse maka Burinka na tsananin bukatuwarka zuwa Gareni in shiga hakkinka,

 Shine ya sanya na jinkirta har sai da ka samu nitsuwa sai lamarin yafi karfin zuciya ta yanzu kuka ya kufcemin ban Shirya ba, 

Allah Sarki lokaci guda naji tausayin ta da mamakinta ya kamani muka tafi gidan su lokacin har anyi mata Sallah an tafi makabarta nan take na bisu wannan Al’amari wallahi ya jima yana bani mamaki nace Ayya kuwa a wannan zamanin za’a samu irin MATATA…….. ❔

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button