Kannywood

Kyawun tafiya dawowa: Bayan shekaru 12 da rasuwar mijinta jaruma Hafsat Shehu ta dawo harkar fim

Hafsat Shehu matar marigayi Ahmad S. Nuhu ta dawo harkar fim bayan shekara goma sha biyu da rasuwar mijinta

– Tun bayan rasuwar mijinta jarumar ta ajiye harkar fim a gefe ta koma kasuwanci, daga baya dai ta sake aure amma bai dore ba

– Yanzu dai an gano hoton jarumar a jikin wata sabuwar fastar fim din da Adam A. Zango zai yi mai suna ‘Basaja Sabon Labari’

Fitacciyar jarumar da tayi shuhura a shekarun baya kuma mata ga marigayi jarumi Ahmad S. Nuhu wato Hafsat Shehu ta dawo harkar wasan fina-finan Hausa na Kannywood bayan shekaru goma sha biyu da rasuwar mijinta.

Jarumar dai ta taka muhimmiyar rawa a fina-finai masu tarin yawa a shekarun baya, kuma mafi yawan fina-finan tayi su ne tare da marigayin mijin nata Ahmad S. Nuhu, inda daga nan soyayya ta shiga tsakaninsu har ta kai su ga yin aure.

Bayan ‘yan watanni da daura auren jaruman Allah ya yiwa jarumi Ahmad S. Nuhu rasuwa.

Tun bayan rasuwar jarumin Hafsat ta tarkata harkar fim ta ajiye a gefe, inda ta mayar da hankali kan harkar kasuwancinta, daga bisani kuma ta sake aure, sai dai kuma auren bai dore ba.

Wata majiya ta bayyana cewa Hafsat ta nuna sha’awarta ta dawowa harkar fim, amma jarumi Ali Nuhu ya bata shawarar kada ta dawo, inda kuma ta dauki wannan shawara tasa ta hakura da harkar har ya zuwa wannan lokacin.

A yanzu dai jaruma Hafsat Shehu ta canja shawara, inda aka ga hotonta a fastar sabon fim din da Adam A. Zango zai yi kwanan nan, mai suna ‘Basaja Sabon Labari’.

Sabon fim din dai ya kunshi jarumai mata da yawa irinsu Zpreety, Halima Atete, Bilkisu Shema, Hafsat Shehu da sauran jarumai mata.

Tuni dai al’umma suka fara bayyana ra’ayoyinsu kan wannan shawara da jarumar ta yanke na dawowa harkar fim, inda wasu ke ganin rashin dacewar hakan, wasu kuma na ganin hakan da tayi daidai ne, tunda harka ce ta nema, idan bata yi ba babu mai bata ko sisin kobo.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button