Labarai

Kalli hotunan bikin Gasar Hikayata ta BBC ta bana 2017

Kalli hotunan bikin Gasar Hikayata ta BBC ta bana
Gidan yada labarai na BBC Hausa ya karrama matan da suka lashe Gasar Hikayata da aka gudanar kan kagaggun labarai a bana.


Maimuna da Balkisu da Habiba da kuma Hindatu wadanda suka lashe Gasar Hikayata ta shekarar 2017

An gudanar da bikin karrawar ne a otel din Sheraton da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ranar Juma’a

Wannan ne karo na biyu da BBC ta sanya gasar kagaggaun labarai ta mata zalla

Bikin ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen Najeriya

Shugaban Sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh yayin da yake gabatar da jawabi a zauren taron

Shugaban ya ce ana aikin yin wani kundi wanda za a wallafa kuma zai kunshi labarai da suka yi zarra a bara da kuma bana

Bikin ya samu halartar tsohon Shugaban Sashen Hausa na BBC Mansur Liman

A bara ne aka fara kirkiro Gasar Hikayata ta mata zalla


Maimuna Idris Sani Beli, wadda ta zama gwarzuwar gasar a bana, ta samu lambar yabo da kuma $2,000


Balkisu Sani Makaranta ce ta zo ta biyu, kuma ta samu lambar yabo da dala $1,000


Habiba Abubakar da kuma Hindatu Sama’ila Nabame Argungu (daga dama), wadanda suka yi na uku, sun samu lambar yabo da $500

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button