Yanzu Yanzu: An ga wata, gobe Take Sallah A Saudiya
Ta tabbata gobe Talata take Sallah yayin da sabon jaririn watan Shawwal ya bayyana a kasar Saudiya. Hakika gobe ne 1 ga watan Shawwal na shekarar Alif dubu daya da dari hudu da arba’in bayan hijirar fiyayyen Halitta daga birnin Makkah zuwa Madinah.
A gobe da ta kasance Talata, 4 ga watan Mayun 2019, za a gudanar da shagulgula na bikin karamar Sallah a kasar Saudiya yayin da jaririn watan Shawwal ya bayyana a Yammacin yau bayan an kai azumi na ashirin tara.
Ko shakka ba bu addinin musulunci ya shar’anta yin azumin farilla na tsawon kwanaki ashirin da tara ko kuma talatin a watan Ramadana inda kuma ake gudanar da bikin karamar Sallah watau Eid Ul Fitr yayin da watan jinjirin watan Shawwal ya bayyana.
A yayin da al’ummar Musulmi ke kirdado tare da laluben bayyanar sabon watan Shawwal a Najeriya, a yau ne za a kai azumi na 29 a wannan mafificin wata na Ramadana da aka fara gudanar wa tun a ranar 6 ga watan Mayun 2019.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya hori al’ummar musulmi a Najeriya da su zura idanu tare da fita wajen laluben jaririn Shawwal daga yau daren Talata.
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.



![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




