Madallah : Ana cigaba da samun saukin farashin abinci a wasu kasuwanni


Alhamdullahi komai yayi tsanani maganinsa Allah irin yadda anka sha tashin gwauron zabi na farashin abinci muna kawo muku rahoto to yanzu kam alhamdullahi sauki sai ƙara samu wa yake daga wajen Ubangiji fatan mu Allah ya kara saukar da farashin abinci kuma ya baiwa mutane halin saye domin zuwan watan rahama watan Ramadan.
Ana ci gaba da samun sauƙin kayan Abinci a kasuwannin jihar Katsina
Kasuwar garin Dandume, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara fara – 51,000_ 52,000 ja – 52,000
2- Buhun Dawa – 47,000
3- Buhun Gero – 57,000 Dauro – 57,000
3- Buhun Gyada tsaba – 100,000 mai bawo – 27,000
4- Buhun Shinkafa tsaba – 115,000 ta tuwo – 120,000 shanshera – 38,000
5- Buhun Wake – 85,000 ja – 100,000
6- Buhun waken suya – 57,000
7- Buhun Dabino – 142,000
8- Buhun Dankali – 21,000
9- Buhun Tattasai – 10,000 kauda- 80,000
10- Kwandon Tumatur kauda – 60,00,000
11- Buhun Tarugu – solo – 45,000
12- Buhun Albasa – 25,000
13- Buhun Kubewa busassa – 35,000
14- Buhun Barkono – 45,000
15- Buhun Alkama – 60,000
Kasuwar garin Dutsanma ,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara – 58,000 _ 60,000
2- Buhun Dawa – 48,000 _ 50,000
3- Buhun Gero – 52,000 _ 54,000
4- Buhun Shinkafa – 100,000 _ 140,000
5- Buhun Gyada kyalla – 115,000
6- Buhun wake – 78,000 _ 80,000
7- Buhun Waken suya – 56,000 _ 58,000
8- Buhun Tattasai – 28,000
9- Buhun Tarugu – 13,000 _ 26,000
10- Buhun Barkono – 44,000
Kasuwar garin ‘Yarlaraba a karamar hukumar Malumfashi,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara – 48,000 _57,000
2- Buhun Dawa – 48,000
3- Buhun Gero – 52,000
4- Buhun Dauro – 53,000
5- Buhun Shinkafa tsaba – 115,000 shenshera – 40,000
6- Buhun Gyada ‘yar Dakar – 110,000 mai bawo – 28,000
7- Buhun Wake – 78,000
8- Buhun waken Suya – 52,000
9- Buhun Rogo – 47,000
10- Buhun Alkama – 60,000
11- Buhun Tattasai solo – 30,000
12- Kwandon Albasa – 35,000
13- Buhun Tarugu – 75,000
14- Buhun Garin kwaki – 40,000
15- Buhun Barkono – 45,000
16- Buhun kalwa – 60,000
17- Buhun Sobo – 26,000
18- Buhun kubewa – 50,000
Kasuwar garin Bindawa, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara – 56,000
2- Buhun Dawa – 44,000
3- Buhun Gero – 48,000
4- Buhun Shinkafa – 100,000 samfarera – 38,000
5- Buhun Gyada tsaba – 105,000 samfarera – 38,000
6- Buhun Wake manya – 82,000 kanana 80,000
7- Buhun Waken suya – 60,000
8- Buhun Tattasai danye – 13,000 kauda – 60,000
9- Kwandon Tumatur – 2,500
10- Buhun Tarugu – 20,000
11- Buhun Barkono – 35,000
12- Buhun Garin kwaki ja – 27,000 fari – 25,000
13- Buhun Alabo – 38,000
14- Buhun kalwa – 60,000
15- Buhun Gishiri – 16,000
16- Buhun Barkono – 45,000
17- Buhun Kanwa 12,000
18- Buhun Goro – 170,000 _ 180,000
Daga Aysha Abubakar Danmusa.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




