Matsin rayuwa: Ban yi nadamar zaɓen Tinubu da Shettima ba — Sheikh Jingir


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Yahaya Jingir, ya ce duk wanda ke jiransa ya yi nadamar matakin da ya dauka na goyon bayan tikitin takarar Musulmi da Musulmi to ya na wahalar da kansa.
A zaben shugaban kasa na 2023, fitaccen malamin addinin musuluncin na Jos ya yi tallan ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a lokacin, Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima, wadanda dukkansu musulmi ne.
Sai dai da ya ke jawabi ga wasu mutane, Sheikh Jingir ya caccaki wadanda ke sukar sa saboda goyon bayan tikitin Tinubu/Shettima.
Sai dai a yayin da yake mayar da martani game da tabarbarewar tattalin arziki da ƴan Nijeriya ke fuskanta a karkashin gwamnatin Tinubu, Jingir ya yi kakkausar suka ga wadanda su ke sukar sa da cewa ya sa sun yi zaben tumun dare.


Daily Nigerian hausa ta ruwaito cewa,Sheikh Jingir, wanda kuma shi ne jagiran wani ɓangare na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, JIBWIS, ya kuma ayyana masu sukarsa a matsayin munafukai.
A cewarsa, babu wani wahala da mulkin Tinubu ya haifar da zai sa ya yi nadama a kan zabin sa.
“Wadanda ku ke zagina ba gaira ba dalili saboda goyon bayan tikitin musulmi da musulmi, makaryata ne; ba ku ma zabe shi ba.
“Suna cewa shi (Tinubu) yana son ya mayar da Abuja zuwa Legas. Ni ne na ba shi shawarar ya yi haka?
“Na goyi bayan takarar Musulmi da Musulmi kuma na gaya wa Tinubu ya yi adalci. Na yi masa addu’ar Allah ya ba shi lafiya, ya kuma yi nasara a zabe, ya kuma samu nasarar,” inji shi.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



