Labarai

Zan kayar da Buhari cikin sauki a zaben 2019 — inji AtikuTsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yace kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari shi yafi komi sauki muddin suka kara a zaben 2019.

Mista Abubakar ya yi wannan ikirarin ne a hirarsa da Dele Momodu na jaridar the Boss.
Atiku yace bashi da haufi ko shakka cewa zai iya kayar da Buhari a zabe domin farin jininsa ya ragu sosai sakamakon kasa cika alkawurran talakawa kamar yadda sukayi tsammani.
Yace shugaba Buhari ya kasa tabuka abun komi tunda ya hau mulki kuma baya tafiya da matasa a mulkinsa gashi cen ana sayar da yan Nigeria kamar awaki a matsayin bayi a kasashen waje.
“Ina da tabbacin ni na shirya tafiyar da Gwamnati daga ranar farko da aka zabeni na hau karagar mulki” inji Atiku

Sources:premiertimes

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button