Subhanallahi ! ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama Da Ashirin A Jihar Zamfara (Hotuna)
Daga Abubakar Kawu Girgir
Mazauna garin Ruwan Tofa cikin ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara sun shiga cikin tashin hankali bayan ‘yan fashin daji sun yi wa yankinsu tsinke tun a ƙarshen makon jiya.
Bayanan baya-bayan nan daga jihar na nuna cewa akalla mutum 21 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin ‘yan fashin daji a ranar Asabar.
Mutanen garin sun ce mahara fiye da 200 ne a kan babura suka auka wa garin tare da buɗe wuta kan mai uwa-da-wabi lokacin da suka yi yunkurin artabu da su.
Wani mutumin Ruwan Tofa ya shaida cewar daga cikin mutanen da aka kashe har da wata mace ɗaya, da kuma namiji 20, yayin da aka jikkata ƙarin mutum goma sha biyar.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara dai ta ce zuwa yanzu ta tabbatar da mutuwar mutum goma ne sakamakon wannan hari na yammacin Asabar.
Shafin rariya na wallafa a shafin Facebook