Labarai

Kissar wanda ya musuluntar da mutane 500 a kurkuku – Dr.Abba idris

Advertisment

Allahu Akbar, Allah ya kan jarabi bayinsa idan sunkayi hakuri sai abun ya zamo musu alkhairi kissar wannan wani bawan Allah ne da wasu sunka musulunta ta hannunsa a kurkuku wanda tabbas wannan babban jihadi ne, duba da cewa mutum ɗaya ya musulunta ta hannunka yafi zama alkhairi a gareka fiye da a baka duniya da abinda ke cikinta.

Babban malamin nan Dr. Abba Idris adam mai kawo muna kissa daban daban da suke dauke da darasi na rayuwa yazo mana da labarin wani bawan Allah da ya samu wata falala ta musamman a tare da shi a lokacin da anka kai shi kurkuku ga yadda labarin wannan bawan Allah ya fara.

Kissar wanda ya musuluntar da mutane 500 a kurkuku - Dr.Abba idris
Kissar wanda ya musuluntar da mutane 500 a kurkuku – Dr.Abba idris

Sunansa yaseer albahri dan kasar kuwait ne ya tafi kasar amerika karatu a shekara ta 2001 daga nan yayi amfani da wannan ya buɗe wajen shan shayi, kasuwa ya samu cigaba ya dauki mutane aiki, a shekara ta 2007 sai wata ma’aikaciyarsa yar amurika ta kirawo masa jami’an tsaro ƴansanda tace yayi ƙoƙari yayi lalata da ita ‘fyade’ aka je kotu aka tabbatar da dukkan hujjoji da za’a bayar babu hujja.

Sai ga CCTV kamara aka nuna a lokacin da tace abun ya faru, aka duba bai faru ba, amma duk da hana juri suka ce baza su barshi ba, aka turashi kurkuku na shekara goma sha biyar 15, yace a zaman da yayi a kurkuku ankaishi kurkurku daban daban guda bakwai, yace a zamansa na kurkuku wanda dukkan musulmi ya kamata yayi kuyi da shi.

Me yayi a kurkuku?

 

A shiga yin da’awa a cikin kurkuku Mutanen da basu san minene musulunci ya nuna musu musulunci a taƙaice dai kafin ya fita sai da mutum ɗari biyar 500 sunka musulunta a hannunsa Allahu Akbar.

Abu na biyu da yayi.

 

A bude dakin ajiyar littattafai ‘library’ guda takwas a cikin gidan kurkuku daban daban Allahu Akbar, an kama shi an masa ƙage amma sai ya juyar da wannan abu ya musuluntar da mutane ta hanyar da’awa, hukumomin ƙasar Amurika sunka yakamata a sallami wannan bawan Allah domin idan ba’a sallame sa ba, domin akwai yiyuwar idan ba’a sallame sa ba dukkan kurkurku da aka kaishi zai iya musuluntar da su Allahu Akbar“.

Yan uwana mutane nawa ne suke da ikon yin wa’azi basuyi ba, yana da mu yi kwaikwayo da irin dabi’u na yaseer albahri, Allah ya sakamasa da macicifin alkhairi, mu kuma ya bamu karfin gwiwa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button