Wani Jigon APC Ya Nemi A Kama Duk Ministocin Buhari Da Hadimansa
Wani jigo a jam’iyyar APC, Dr. Garus Haruna Gololo, ya yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) da su cafko tare da gurfanar da duk wasu tsoffin ministocin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Gololo, wanda ya bayyana hakan a Abuja ranar Lahadi yayin da yake zantawa da manema labarai, ya kuma bukaci hukumomin da su bi duk wasu na hannun daman tsohon shugaban kasar, wadanda suke da hannu kan badakalar shari’ar da ta dabaibaye tsohon shugaban Babban bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele.
In ba a manta ba, kodinetan kungiyar HURIWA na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya taba yin Allah-wadai da shirin sake fasalin takardun Naira, inda ya yi zargin cewa, shirin ya fito ne daga hadimin Buhari, Sabiu Tunde ‘Yusuf, jaridar Liberty tvr na ruwaito.
Dr. Gololo ya ce, Emefiele a halin yanzu yana kan shari’a, amma me ya hana EFCC ko DSS gayyatar Sabiu domin yi masa tambayoyi?
Ya kamata a binciki tsoffin ministocin musamman ma’aikatar kudi, jin kai, sufurin jiragen sama, sufuri da sauransu kan harkokin kudi a lokacin da suke kan madafun iko.