Rabi’u Rikadawa “Dan Audu” Ya Zama Gwarzon Jarumin Kannywood Na Shekarar 2023
Fitaccen dan jaridar nan kuma marubuci Ahmad Nagudu ya wallafa wannan rubutu na cigaba da nasarar da fitaccen jarumin nan ya samu Rabiu Rikadawa wanda yayi fice da dan audu a cikin shirin labarina mai dogon zango.
An karrama jarumin Kannywood, Rabi’u Muhammad Rikadawa da kambun gwarzon jarumin Kannywood na shekarar 2023 a Abuja.
Ita dai wannan lambar yabo (Award) wadda Mujallar OurNigeria News da ke lamba 2 Gwari Street, City Library, Wuse Zone 4, Abuja, ta ke shiryawa duk shekara, ta zabo tare da bawa jarumi Rikadawa wannan Kambun Gwarzon Jarumin ta daga Kannywood na shekarar 2023 ne ta la’akari da muhimmiyar gudummowar da ya ke bayarwa wajen hadin kan Najeriya da kuma ci-gaban rayuwar al’umma.
A wani zama da Hukumar Gudanarwar Mujallar OurNigeria News ta gudanar a ranar 25 ga watan Yulin shekarar 2023, ta gamsu tare tabbatar da ra’ayoyin da mafi yawan masu karatun ta su ka bayyana kan cancantar jarumi Rabi’u Rikadawa a matsayin Gwarzon Jarumin ta na Shekarar 2023.
Kambun Gwarzon Jarumin Shekara na daga cikin kyauta mafi girman daraja da Mujallar OurNigeria News ke bawa mutanen da su ka nuna wani lamari na daban na kwazo da yabawa cikin al’umma.
An dai gudanar da taron bayar da kambun karramawar ga jarumi Rikadawa ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwambar 2023 a babban dakin taro na kasa (ICC – International Conference Centre) da ke babban birnin Tarayyar Najeriya Abuja.
Asiya Barade ita ce kawai daga cikin yan Kannywood ta samu halartar taron sai kuma wasu daga cikin abokan jarumi Rikadawa tun na kuruciya da su ka kasance da shi yayin ba shi kambun.