Labarai
Hadimin gwamna Ganduje, Yakasai ya caccaki Shugaba Buhari kan rikicin Yarbawa da Hausawa a Oyo


Advertisment
Hadimin gwamnan Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan rikicin Hausawa da Yarbawa a Oyo.
A yace rubutun da shugaban kasar yayi a shafukan sada zumunta sun yi kadan su magance matsalar.
Yace ya kamata shugaban kasar ya dauki mataki da gaggawa kamin lokaci ya kure.
Hutudole ne na tattara bayyanai.A baya dai Gwamnan Kano ya taba dakatar da Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rikicin Hausawa da Yarbawa a Oyo ya dauki hankula sosai inda ya saka fargaba a garin.