Wata budurwa ta yiwa su ado Gwanja wankin babban bargo akan wakar chass
Wata budurwa a shafin sada zumunta na Tiktok ta fito karara ta bayyanawa duniya cewa tayiwa Ado Gwanja aikin bidiyon wakar Chass amma sun hanata haƙƙinta dashi da wanda ya bada umarnin bidiyon (Umar MB)
Matar ta kara da fadin a ranar ankirawota ne da zummar zatayi aiki a biyata,sannan ta kara da fadin kuma tana Azumi a ranar,har akasha ruwa bata tsaya tasha ba inda take cewa a cikin bidiyon.


” Fine up an saki wakae chass umar MB you shall Thank GOD banda Face dina ba, dan wallahi daman jira nake naga an saki full wakar chass banda ga alart ba banga hakkina ba hmmm da wannan lokaci ka taba wanda tasan incin kanta tasan me take yi inga fuskata a wakar kuma banga alart ba, ba’a biyani hakkina ba yi hakuri wallahi da ka tantance wanda ta fito business din ba wadda ta fito selling kanta ba.
Ka gode ma Allah kayi deleting dukka inda nake a ciki if not sorry da kaga inda ake zuwa a kwaci hakki na rantse maka da Allah umar MB ku dinga biyan mutane hakkinsu saboda gashin nan kunki samun daukaka saboda baku biyan mutane hakkinsu ku dinga fadin wai favour kunkayi masa.
Budurwa ta kara da cewa a lokacin da za’a yi wakar tana azumi tace Tk ana biya yace haba haba ana biya mana wakar ado Gwanja ce fah, to ni ba damuwa ta wai ta Ado Gwanja bane an sanin shi a’a ni kudi nazo nema shine business dina
Daman yaran da anka sanya wadanda suna kuri sunyi waka da ado Gwanja ni bai dame ni ba, ba yau nasan ado Gwanja ba ba ruwana da shi.
A ranar da ankayi ina azumi banyi cikakken ibada ba, ban tsaya nayiwa kaina addu’a mai kyau ba saboda ina neman hakkin na wuni can har dare ko ruwa mai kyau ban sha ba.”
Ga bidiyon nan ku saurara kuji daga bakinta daman hausawa kance waka a bakin mai ita yafi ɗaɗi da tashar YouTube D-kannywood na kawo.
To ita wannan budurwa miya kaita hawan irin wannan wakar bayan yana dauke da azumi wanda zatayi jirgiza jikinta azumi ana so mutum yayi istigifari da sallati da karatun Alqur’ani.






