Kannywood

Bayan Kujerar Hajji harda Mota Dr Idris ya bani cewar Aminu J Town

Aminu J Town wani matashi da a kwanakin baya yayiwa Ƴan fim kaca-kaca ko kuma ace tonon silili ya fito ya bayyanawa duniya cewa bayan kyautar Kujerar Hajji harda sabuwar mota Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya bashi bayan fede biri har wutsiya da yayi.Bayan Kujerar Hajji harda Mota Dr Idris ya bani cewar Aminu J Town

Aminu J Town din wanda ya bayyana a wani labari daya saka a shafinsa na Tiktok,Aminu din yace Malamin yayi masa kyautar Motar ne bayan da aka kai mishi hari a Abuja aka faffasa masa gilashin motar bayan sakin bidiyon sukar da yayiwa Yan Fim.

Haka kuma ya kara da cewa akwai wata mata da yarta daya ceto bayan da yarinyar da tuni ta zuba kudin gadon su har miliyoyi a harkar fim.

Yace Mahaifiyar yarinyar bayan taga bidiyon sa ta hana yarta ta,sanan bugu da kari tayi masa godiya mara misaltuwa.

Kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button