Labarai

Bayan shekaru 2 da Rabuwar su budurwa ta karbo motar da ba ta baiwa saurayinta kyauta

Wata budurwa ta tada kura a dandalin soshiyal midiya na TikTok bayan wallafa irin tarkacen da ta gani a motarta da ta dade a hannun tsohon saurayinta.

Ta wani shafin TikTok @diahy.fox, ta nuna yadda cikin motar ya kasance, wanda ke nuna yadda hunhuna ke cigaba da rayuwa a wurare daban-daban a ciki.legit na Ruwaito

Sauran bidiyon da ta dauka sun nuna yadda motar ta fito fes wacce ta bayyana yadda aka dauki tsawon awanni uku ana kankarewa gami da wankewa.

Bayan shekaru 2 da Rabuwar su budurwa ta karbo motar da ba ta baiwa saurayinta kyauta
Bayan shekaru 2 da Rabuwar su budurwa ta karbo motar da ba ta baiwa saurayinta kyauta

“Se da na dauki tsawon awanni uku wajen kwashe dattin motar.”

– Tace.

An tambayeta dalilin barin motar na shekaru 2

Yayin da masu amfani da yanar gizo suka tambayi dalilin da yasa ta dauki tsawon lokaci kafin amsar motarta, ta sake yin wani bidiyo inda ta bayyana:

“Muna tare lokacin da motarsa ta lalace. Kawai nayi kokarin nuna masa mutuntaka ne, budurwa mai kima… Na taimakesa.
“Kun san idan kana son mutum za ka yi iya kokari don taimaka masa. Amma bayan mun rabu, ba naso in yi harkar karanta ko in kuntatawa rayuwarsa. Duk da haka ina so ya samu aiki sannan yayi rayuwa mai dadi.
“Hakan ne dalilin da yasa yayi amfani da ita tsawon shekara bayan mun rabu..”

Martanin jama’a

Relichunter37814 ta ce:

Za ki iya bincikar dalilin da yasa ta zama haka, amma za ki iya maka shi kotu gami da bukatar wasu kudi.”

Sarah ta ce:

“Rai na gaba daya ya baci kuma na daburce. Yadda na gyara motar har tayi kyalli gami da wallafa ta.”

Wind S ya ce:

“Yarinya, ki fada min baki biyan inshoran wannan? Idan da ni ne ai da na kira su nace tsohon saurayina ya sace min mota.”

sav ya ce:

“Wannan ai abun kunya ne gare shi, wai me ma yake yi ne.”

Isaac Pando ya ce:

“A matsayina na wanda ya duba motar da kyau, zan ji kamar ana tsingulina idan na fara amfani da motar. Ki kai ta wajen kwararre, na miki alkawari kashi 99.9 na barnat zai tafi.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button