Abin Al’ajabi :Jaririn da aka haifa da hannaye hudu da kafafu hudu (hotuna)
An bayyana wani jariri da aka haifa da hannu hudu da kafafu hudu a matsayin “abin al’ajabi na dabi’a” a Indiya.
An kuma kwatanta yaron da mutum mutumi mai siffar dabbobi da Allah hallita a cikin mutane.Hotunan yaron da aka haifa a karshen mako a Hardoi da ke arewacin kasar, an yada su a yanar gizo.jaridar LIB na ruwaito

Yana nuna jaririn tare da ƙarin gaɓoɓi huɗu da ke manne a ciki.
Yaron yana da nauyin kilo 6.5 kuma an haife shi a Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama’a ta Shahabad, a jihar Uttar Pradesh.

An garzaya da mahaifiyar jariri mai Kareena asibiti bayan ta yi fama da ciwon nakuda a ranar Asabar 2 ga watan Yuli, kuma ta haihu ba da jimawa ba.

Jama’a sun yi ta tururuwa domin ganin ta bayan labarin ya bazu a yankin kuma mazauna yankin sun kwatanta jaririyar da wata baiwar Allah mai kafafuwa da dama
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



