Labarai
An Kaddamar Da Gangamin Tazarcin Buhari A Jihar Ebonyi
Jam’iyyar. APC reshen jihar Ebonyi ta kaddamar da wani gangami a garin Abakaliki na murnar dawowar Shugaba Buhari daga jinya da kuma fara nema masu goyon baya don yin tazarce a shekarar 2019.
Shugaban jam’iyyar, Eze Nwachukwu ya ce wannan shi ne karo na uku da ake gudanar da irin wannan gangami na nuna soyayya da goyon baya ga Shugaba Buhari inda ya kuma yabawa ‘ya’yan jam’iyyar kan yadda suka bayar da hadin kai wajen samun nasarar gangamin. Daga cikin wadanda suka halarci gangamin akwai, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu da kuma tsohon Gwamnan jihar, Martins Elechi.
Sources:Rariya