Isra’ila ta lalata masallatai sama da 1,000 a Gaza da hallaka masu wa’azi sama da 100
Isra’ila ta lalata masallatai 1,000 a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
“Sake gina wadannan masallatan zai ci kudi kimanin dala miliyan 500,” kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Addini da ke Gaza ta bayyana a wata sanarwa.
TRT Afrika hausa na ruwaito cewa akwai kimanin masallatai 1,200 a Zirin Gaza. Ma’aikatar ta ce Isra’ila ta kashe malamai masu wa’azi sama da 100 tun bayan soma wannan yakin.
Wani Labari :Yunwa da kishirwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana
Hare-haren da Isra’ila ta kwashe sama da wata biyu tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 17,487, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 46,480 sun jikkata.
Falasdinawa dubu 500 ke cikin barazanar yunwa da kishirwa a biranen da hare-haren Isra’ila ke kara karuwa, kamar yadda gwamnatin Gaza ta bayyana.
Jaridar trtafrika na ruwaito Gwamnatin ta Gaza ta ce jama’ar birnin na cikin bala’i sakamakon dagangan Isra’ila ke kai hare-hare kan ababen more rayuwa da ke da alaka da abinci da ruwa.
Mai magana da yawun birnin, Hosni Muhanna ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar cewa karancin man fetur yana kawo cikas wurin kwasar wadanda suka samu rauni da kuma jigilar gawawwaki.