Nigeria vs Ghana : Magoya bayan Super Eagle Sunyi Sanadiyar Ajalin wani Likita
Kamar yadda Daily Trust suka ruwaito, Magoya bayan Super Eagles sun yi ajalin wani likita dan asalin kasar Zambiya bayan da suka lakada masa dukan kawo wuka, bayan tashi daga wasan Najeriya da Ghana a Abuja kamar yadda datti assalafy ya ruwaito.
Joseph Kabungo likita ne daga cikin jerin wadanda Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF), ta tura Abuja don sanya ido a kan wasan da aka yi tsakanin Super Eagles ta Najeriya da Black Stars ta Ghana ranar Talata
Shine jami’in da CAF ta tura don yi wa ’yan wasa gwajin amfani da abubuwan kara kuzari a wasan Najeriya da Ghana da aka yi a filin wasa na M.K.O Abiola da ke Abuja.
Ya rasu bayan magoya bayan Super Eagles sun fusata tare da shiga cikin filin wasan, rahotanni sun ce magoya bayan sun lakada masa dukan da ya yi sanadin fita daga hayyacinsa.
Daga bisani an garzaya da shi asibiti don ba shi agaji, amma aka yi rashinsa sa’a rai ya yi halinsa.
Wani dan jaridar kasar Zambiya, Matimba Nkonje, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana mutuwar Kabungo a shafinsa na Twitter.
Tawagar ’yan wasan Super Eagles dai ta gaza zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da za a yi a kasar Qatar, bayan yin kunnen doki da Ghana. ~Daily Trust
Kamar yadda na fada jiya, nace ya kamata hukumar kwallon kafa na duniya ta hukunta Nigeria bisa rashin da’a da zin zarafin mutane da suka nuna a wasan jiya, a haramtawa Nigeria shiga harkokin kwallo na tsawon shekaru 50
Ta gashi lamarin yayi kamari, har kisan kai aka aikata, na tabbata Nigeria ba zata tsallake takunkumin hukumar kwallo na Afirka da na duniya ba, kuma wannan abin kunya ne