Labarai
Yan Bindiga Sun Sace Mutane Sama Da 80 A Karamar Hukumar Jibia
Sun Maida Sama Da Mutane 2000 Yan Gudun Hijira
Advertisment
Ƴan Bindiga Su Sama Da 200 A Saman Babura, Sun Kai Wani Mummunan Hari A Kauyen Faru Dake Cikin Karamar Hukumar Jibia A Jihar Katsina. Shafin Katsina post na rahoto
Kamar Yadda Majiyar Mu Ta Tabbatar Yan Bindigar Sun Yi Awon Gaba Da Mata Da Kananan Yara Sama Da Tamanin,Tare Da Kone
Gidaje Da Kuma Maida Sama Da Mutum Dubu Biyu Ƴan Gudun Hijira.
Majiyar Jaridar Focus News Hausa Ta Shaida Mata Cewa, Yan Bindigar Dauke Da Bindigogi, Suka Yi Wa Garin Kawanya Suka Yi Ta Harbin Mai Kan Uwa Da Wabi, Suka Cigaba Da Farfasa Shaguna Tare Da Kone Gidajen Kauyen.
A Halin Yanzu Kimanin Sama Da Dubu Biyu Ke Zaman Gudun Hijira A Garin Magamar Jibia Da Kuma Karamar Hukumar Jibia.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






