Kannywood

Atiku Abubakar Ya Baiwa Jaruma Fati Muhammad Mukami

Advertisment

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake nada jaruma Fati Muhammad a matsayin jakadiya a karkashin kungiyar sa mai suna Atiku Care Foundation.

Fati Muhammad ta kasance daya daga cikin jaruman da su ka taka muhimmiyar rawa a tafiyar Kannywood, kuma ta bada gudunmawa sosai a ci gaban masana’antar.

Tun bayan da jarumar, Fati Muhammad ta dawo daga nahiyar turai ta tsunduma harkokin siyasa, kuma a lokacin ne Alhaji Atiku, ya nada ta a matsayin ambasadar kungiyar sa, sakamakon jajircewar ta tare da nuna kulawa ga harkokin ci gaban mata musamman bada tallafi ga marayu da kuma mabukata.

Har ila yau, jarumar ta tsaya tare da bada gudunmawa da goyon baya a lokacin da Alhaji Atiku Abubakar yake neman kujerar shugabancin kasar nan.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button