Kasar Amurka Ta Baiwa Nijeriya Taimakon Dala Miliyan 33 Domin Cigaba Da Yaki Da Cutar Corona
Daga Comr Abba Sani Pantami
Gwamnatin kasar Amurka ta baiwa Nijeriya kyautar zambar kudi $33m, kimanin naira biliyan 12.89 kenan a matsayin tallafin yaki da annobar Coronavirus a kasar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Jakadiyar Amurka a Nijeriya, Mary Beth Leonard ce ta bayyana haka a ranar Laraba yayin hira da ta yi a wani gidan rediyo Lagos Talk 91.3FM.
Mary ta ce zuwa yanzu Amurka ta tallafa ma kasashen duniya da dama da kudi dala biliyan 2, duk a kokarinta na ganin an hada karfi da karfe wajen shawo kan cutar.
Haka zalika ta kara da cewa Amurka da Najeriya na cigaba da tattaunawa a tsakaninsu domin fadada hanyoyin da za su bi wajen yaki da cutar.
Mun baiwa Najeriya dala miliyan 33 don yaki da COVID-19, muna kuma lalubo hanyoyin da za mu bi don hadin gwiwa da juna, muna kuma lura da yadda ake kula da marasa lafiya a kasashen biyu.

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)







