Labarai

Yanzu – Yanzu : Rundinar Sojojin Nigeria Ta Yiwa Gwamna Zulum Raddi

Advertisment

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron sojin Nigeria Manjo Janar John Enanche ya mayar da raddi bisa zargin da Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yayi cewa sojoji ne suka kaddamar masa da harin kwanton bauna lokacin da ya ziyarci garin Baga

Janar Enanche yace ‘yan ta’addan  Boko Haram ne suka kaddamar da harin a kan Gwamna Zulum ba kamar yadda shi Gwamnan yayi zargin cewa sojoji ne suka masa hari ba

Janar Enenche yace ganin zargin na Gwamnan na da girma sosai, ba su bata lokaci wajen gudanar da bincike a kai ba, kuma bayanan da suka tattara ya tabbatar musu cewar babu hannun wani soja cikin wadanda suka kai masa hari a garin Baga

Mai magana da yawun ma’aikatar tsaron sojin yace; sun bi matakai da dama wajen tabbatar da wannan matsayi da suka hada da bidiyon da aka dauka lokacin harin da inda aka dinga jin karar harbe harben, da kuma irin makaman da aka yi amfani da su wajen kai harin da suka sha banban da na sojin.

Janar Enenche yace don haka babu gaskiya kan zargin da aka yi wa dakarun sojin Nigeria wadanda suka sadaukar da rayukan su domin kare lafiyar jama’ar Nigeria, inji Janar Enanche

Nigeria kenan, ta bakin Maimartaba Shehun Borno yace indai babban mutum kamar gwamnan Borno bai tsira ba to babu wanda ya tsira, nayi imani da Allah Gwamna Zulum ba zai fito yayi irin wannan zargi ba tare da yana da hujja mai karfi ba

Kuma abinda ake fadawa ‘yan Nigeria a baya shine an kwato garin Baga, baya hannun Boko Haram, to suwaye suka yi masa hari lokacin da ya shiga garin Baga tunda ance babu Boko Haram a garin?, dama karya aka yiwa ‘yan Nigeria?

Kuma ai ba wannan bane karo na farko da aka nemi salwantar da rayuwar Gwamna Zulum a Baga ba, maciya amana sun taba neman rayuwarshi a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, har mataimakinshi ma sun taba neman rayuwarshi cikin wannan kulle na Coronavirus da akayi

Ya rage wa ‘yan Nigeria su gaskata Gwamna Zulum ko su karyatashi su gaskata maciya amanar tsaron Nigeria, kuma ya rage wa shugaba Buhari ya rabu da wannan miyagun mutane maciya amana ko ya kyalesu tarihinsu ya lalace gaba daya bayan shekarar 2023

Yaa Allah Ka kare Gwamna Zulum daga dukkan sharri da makirci, Ka cika masa burinsa na ganin karshen bayan Boko Haram da maciya amanar tsaron Nigeria Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button