Ina kuke Masu Neman Matan Media, wannan darasi ne Gareku
Majiyarmu ta a samu wani labari daga fitaccen marubuci Datti Assalafy ya wallafa a shafin na Facebook yana cewa
Wannn hoto da kuke gani wani yaro ne matashi mai suna Musa Lawan Maje, ita kuma yarinyar da kuke gani budurwansa ne
Musa ya bude Facebook account na bogi da sunan Zahra Mansur, facebook account din ya shahara sosai, ana masa ruwan comments da likes, ya tara followers sama da dubu 32
Musa shi yake gudanar da Facebook account din yana saka hoton budurwansa, ba abinda yakeyi da account din sai zallar damfarar mutane yana karban makudan kudi a hannun maza masu neman matan banza a media
Musa ya saya wa budurwansa babbar waya, ya saya mata layin kiran waya yayi rijista da sunan Zahra Mansur, har bank account sai da ya bude mata da sunan Zahra Mansur domin su damfari wawaye masu kwadayin matan media
Wato wani irin salon damfara yake yi ta hanyar yaudara da sunan soyayya, ya samu nasaran karban hotunan tsairaici na maza ‘yan media masu dumbin yawa a Facebook, a haka yabi ya danawa maza ‘yan media tarko yana karban makudan kudade, har ‘yan mata kwadayayyu bai bari ba, da zaran ya samu hotonka na tsiraici to ya mayar da kai ATM machine
Ni Datti Assalafiy na sha jawo hankalin mutane a wannan kafa na Facebook, ina yawan fada muku cewa kuyi hankali da hotunan ‘yan matan media da kuke gani, muna cikin wani yanayi ne na Artificial Karuwai, suna da salo mabanbanta da suke bi su tatsi kudi a gurin mutanen banza, sannan suna hada kai da kwararrun ‘yan damfara
Yanzu dai asirin Musa Lawan Maje ya tonu, an dana masa tarko kuma an kamashi kamar yadda yake dana wa wasu tarko, yanzu haka yana hannun ‘yan sanda, da aka duba wayar hannunsa anga hotunan tsiraici da bidiyon tsiraici na wasu manyan ‘yan social media masu dumbin yawa, da zamu fitar sai media ta kama da wuta saboda tonon asiri
Imbanda wauta da gidadanci da rashin wayo, haka kawai don kwadayin kyawun fuskar macen da ka gani a media kuka fara soyayya sai ka dauki hoton tsiraicinka ka tura?
Shin Baku san cewa asalin mata kyawawa basa nuna kansu ba? wadannan hotunan mata da kuke gani a media kuke musu ruwan comments da likes adon photoshop application ne, da zaku gansu a zahiri sai kun gudu
Don Allah ‘yan uwa kuyi hankali da matan media, ko da wasa kar ka yadda ka dauki hoton tsiraicinka ka tura da sunan kun kulla soyayya, tarko ne, zata mayar da kai ATM machine idan ka fada tarkon, zata talauta karkatakaf, idan kunne yaji to gangar jiki ya tsira
Allah Ya cigaba da karemu fadawa tarkon mutanen banza
آمين يا رب العالمين