Davido ya cika alƙawarin raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu 292


A ƙarshen 2021 ne Davido ya sanar da cewa zai raba Naira Miliyan 250 ga gidajen marayu a faɗin ƙasa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.
Davido ya baiyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Talata da daddare.
Davido ya bada cikakken bayani da sunayen gidajen marayun da su ka amfana da tallafin na sa, inda ya ce gidajen marayu 292 ne su ka amfana.
Mawaƙin ya kuma gode da yabawa ƴan kwamitin da ya kafa su raba tallafin, inda ya ce kwamiti ne cike da mutane zaƙaƙurai da su ka iya aiki.
Ya kuma yabawa magoya bayansa da danginsadanginsa da kuma abokai.






Gaskia 2k tayi albarka ????kalli sabbin motocin jaruman kannywood na milliyoyin nairori a sabuwar shekarar nan
https://youtu.be/Q46wOmscsc0