Qausain TV ta naɗa Adam A. Zango a matsayin darakta janar


Gidan Talabijin na Qausain TV ya sanar da nada fitaccen jarumin fina-finan Kannywood kuma Mawaƙi Adam A. Zango a matsayin Darakta Janar na gidan Talabijin ɗin.
Shugaban kamfanin Qausain, Alh Nasir Idris ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa naɗin Adam Zango a matsayin Darakta Janar ɗin ya fara aiki nan take.
A cewar sanarwar, an amince da naɗin ne yayin wani taron hukumar daraktocin kamfanin.
Alhaji Idris ya kara da cewa an naɗa tsohon Gwamnan Soja na Jihar Kano, Kanar Sani Bello (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar daraktocin kamfanin.
“Naɗin Bello a matsayin Shugaban hukumar daraktocin kamfanin na tsawon shekaru hudu ne, kamar yadda dokar Kamfanoni ta tanada.
Idris ya ce an naɗa tsohon ministan sadarwa Farfesa Isa Pantami a matsayin mai sanya idanu kan harkokin shugabannin kamfanin.



