Kannywood

Yadda Mansurah Isah ke Rabon kayan Abinci Gida-Gida (A Cikin Hotuna)

Advertisment

A daidai lokacin da a ke tsakiyar bukatar taimako a cikin al’umma, a cikin wannan watan na Ramadan mai tsarki, tsohuwar jaruma Mansurah Isah, a karkashin Gidauniyar ta mai suna Today life Foundation ta ta shi haikan wajen taimako ga mabukata musamman ma dai a wannan lokacin na zaman Covid-19 da kuma Azumi.

Mansurah Isah wadda ta dade a kan irin wannan bayar da kayan tallafin ga mabukata, sai dai a wannan lokacin, abun ya canza Salo, inda baya ga abincin da ta ke dafawa a na rabawa a kullum lokacin buda baki a gidan ta, a yanzu da ta shirya wani tsari na shiga unguwa cikin loko-loko domin raba kayan tallafin har zuwa gidajen mabukata.

A kullum dai a kan dafa abinci a gidanta da kunun tsamiya da na gyada, har ma da ruwa mai sanyi in da mutane su ke zuwa su karba a daidai lokacin shan ruwa, wannan ya sa jama’a masu bukata su ke cika gidan a daidai lokacin shan ruwa domin samun abun buda baki.
Amma duk da hakan Mansurah Isah ta ware wasu ranaku, inda ta ke bi cikin gidaje birni da kauyuka domin raba kayan abinci ga mabukatan.

Wakilin mu da ya ga yadda rabon abincin ya kasance a wata unguwa, ya ga yadda a ke rabawa, Jama’a shinkafa da taliya man girki, wake, garin masara har ma da Dandanon girki, sai a hada a zuba a leda a na rarrabawa mutane. Tun da a ka fara Azumi ne a ke yin wannan aikin na rabon kayan abincin, amma har yanzu a na ci gaba da yi, yayin da hakan ya sa ta ke samun yabo da kuma addu’a a wajen mutanen da su ka samu kayan tallafin.

A lokacin zantawar su da wakilin mu dangane da irin tsarin rabon kayan tallafin na ta na bana. Mansurah Isah ta bayyana cewar.

“Shi wannan rabon kayan tallafin na bana ya bambanta da wanda mu ka saba yi a baya, sakamakon yadda mabukata su ka karu a wannan lokacin, domin haka ne tun da a yanzu a na zaman gida ba a fita saboda halin da mu ka samu kan mu, domin haka sai mu ka yi tsari na bin unguwanni da gidaje, domin kai wa jama’a kayan tallafin, domin haka ka ke ganin mu na bi unguwa-unguwa, har cikin gida mu ke shiga mu sadar da tallafin ga jama’a, kuma wannan abun alfahari ne a gare mu, ganin yadda mutane da yawa ba su da abun da za su ci, saboda ba a fita domin haka mu ka ga me ya kamata mu yi domin faranta wa jama’a, kuma su samu abincin cikin sauki. Hakan ce ta sa mu ke bi gida-gida domin kai wa mabukata”. Inji Mansurah Isah.

Mansurah Isah ta yi kira ga mawadata da su kara rubanya taimakon da su ke yi ga mabukata, domin a yanzu jama’a su na cikin wani hali na bukatar taimako.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button