Kannywood
Bidiyo : Bayan rashin nasarar aure har biyu Fati Muhd ta bayyana burin ta a duniya
Daga bakin mai ita wani shiri ne na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.
A wannan kashi na 35, shirin ya tattauna da shaharrariyar tauraruwar fina-finan Kannywood Fati Muhammad wadda ta amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarta.
A cikin tattaunawar, ta yi waiwaye kan dalilan da suka sanya ta soma harkar fim, da irin rawar da ta fi takawa, da ma wanda ta fi so a hada ta da shi a fim.
Kazalika ta yi magana kan abin da ba za ta taba mantawa da shi ba, da kuma shigarta harkokin siyasa, har ma da nau’in abincin da ta fi so ta ci.
Ga bidiyon nan kasa