Kannywood

Rarara Ya Gina Makarantun primary guda uku A Jahar Katsina (bidiyo da hotuna)

Advertisment

Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Gina Sababbin Makarantun Primary Guda Uku a Jahar Katsina
Ya Gina Daya Acikin Unguwar Da’iya Kahutu
Ya Gina ta Biyu A Gidan Dari
Ya Gina ta Uku A Barmi

Yau Ake Bikin Bude Wadannan Makarantun Karkashin Jagorancin Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Alhaji Dauda Kahutu Rarara

Zamu Kawo Muku Yadda Ake Bikin Bude Wadannan Makaruntu Idan Anjima Insha Allah,kamar yadda Rabi’u Garba Gaya mai taimaka a fannin midiya na ruwaito.

Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Kaddamar Da Bude Sababbin Makarantun Primary Daya Gina Guda Uku Akauyekan Unguwar Da’iya Kahutu Da Gidan Dari Da Kuma Barmi Dake
Jahar Katsina.

Advertisment

Yayin Jawabinsa Ga Al-Ummomin Yankin Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Alhaji Dauda Kahutu Rarara Yace ilimi Shine Ginshikin Al-Umma Saboda Haka Iyaye Su Daure Suna Turo ‘Ya’yan Su Makaranta
Idan Yara Sukayi ilimi Za’a Sami Al-Umma Ta Gari.

Sannan Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Kara Da Cewa Domin Taimakawa Matasan Da Sukayi Karatu Amma Basu Da Aikinyi Yace Zai Dauki Malaman Makaranta a Yankin Guda Dari Uku {300} Domin Taimakon Su
Daga Karshe Mai Girma Shugaban Kasar Mawakan Nigeria Yace Insha Allahu Nan Gaba Zaiyi Kokarin Nema Musu Aiki Na Din-Din-Din a Gwamnati.

Ga bidiyon nan da hotuna.

 

 

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button