An tsare kwamandan sojoji na Kano bisa zargin siyar da shinkafa da kayan sojoji


An tsare kwamandan runduna ta 3 ta sojan Nijeriya da ke Kano, Birgediya Janar M.A. Sadiq, a dakin tsaro na Sojoji da ke Abuja, bisa zargin karkatar da tallafin shinkafa, da sayar da kayan aikin soji da suka hada da jannareto da motocin aiki, ga masu sana’ar gwangwan.
Wasu majiyoyin da su ka zanta da DAILY NIGERIAN, wadanda su ka nemi a sakaya sunansu sun ce, hedikwatar tsaro ta kasa ta bayar da shinkafar ne ga rundunar ta kasa baki daya domin raba wa sojoji a matsayin agajin gaggawa.
DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, hedikwatar tsaro ta raba shinkafar a kalla sau uku ga sojojin Nijeriya, kamar yadda aka tsara.
Janar din da aka kulle, a cewar majiyoyi, ya raba shinkafa mai nauyin 5kg sau daya maimakon sau uku ga sojojin sannan ya sayar da sauran.
Baya ga badakalar shinkafa, DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, Janar din ya kwashe kayan aiki da su ka hada da janaretan MIKANO a sansanin horas da sojoji da ke Falgore a Kano ya sayar da su ga dillalan ‘yan gwangwan.
DAILY NIGERIAN ta tabbatar da cewa, an maye gurbin wanda ake zargin da wani tsohon magatakarda na Kwalejin Tsaro ta Nijeriya, Birgediya Janar A.M. Tukur.
Kakakin Rundunar Sojin Nijeriya, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, bai amsa kira da sako ta wayar da aka aika zuwa ga lambar wayarsa da aka san shi ba a lokacin rubuta wannan rahoto.