Labarai

[Bidiyo] Sojoji , ‘yan sanda tare da ‘yan sakai da ‘yan banga sun hallaka ‘yan bindiga sama da 100 A Garin Bangi

“Rahotanni dake fitowa daga garin Bangi hedikwatar ƙaramar hukumar Mariga, na tabbatar da Allah ya baiwa jami’an tsaro da ‘yan banga/Sakai nasarar fatattakar ayarin ‘yan bindigar da suka afkawa ofishin ‘yan sanda na garin.
Bayanai sun nuna cewar an hallaka ‘yan bindigar dadama tare da ƙwace baburan da ake kyautata zaton sun kai ɗari da makaman su, wanda ake hasashen kusan dukkan ‘yan bindigar da suka yi yunƙurin kai wannan harin babu wanda ya tsira sai wanda kila kwanan sa bai ƙare ba a cikin su. Kuma bayanai na nuni da sune waɗanda suka kashe mana hazikin ɗan sanda CSP Dakingari da wasu jami’an tsaron mu a Nasko.
Nasarar hakan dai ya samu ne sakamakon bayanan sirrin da jami’an tsaron suka samu inda suka kwantawa barayin, lamarin da ya kai ga samun nasarar ragargazar su. Al’ummar garin na Bangi da kewaye sun yaba matuƙa da ƙoƙarin jami’an tsaro akan wannan al’amari tare da addu’o’in ƙara samun nasara akan waɗannan azzalumai.
Ƙarin bayani na tafe Insha Allah.
Muna roƙon Allah ya ƙara basu nasara
Comrd Zakari Ya’u Kontagora.”
Bayan wanna rahoto da yakawo ya sake wallafa wani faifan bidiyon inda mutanen garin cikin bidiyo suna murna irin fatatakar yan bindiga da sunka irin yadda sunka samu nasara akansu.
“MURNAR NASARAR FATATTAKAR ‘YAN TA’ADDA:
Al’ummar garin Bangi dake ƙaramar hukumar Mariga kenan, suka fito murnar nasarar da jami’an tsaro suka samu na hallaka gwamman ‘yan bindiga da yammacin yau.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button