Labarai

Kotu ta yi hukuncin ɗaurin shekara 7 ga wani dan Kano mai shekaru 48 da haihuwa saboda safarar wata yarinya ‘yar shekara 16

Wata kotu da ke zama a jihar kano ta yanke hukunci wani daurin shekara 7 wanda marubucin nan Aliyu Samba a shafin ya ruwaito.

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani mutum mai suna Muhammed Idris mai shekaru 48 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari a ranar Litinin bisa samunsa da laifin safarar mutane.

Mai shari’a Jane Inyang ta yanke hukuncin ne bayan Idris ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma kotun ba ta bai wa Idris wani zabin biyan tara ba.

Tun da farko dai mai gabatar da kara Nuruddeen Hussain, ya shaida wa kotun cewa wanda aka yanke wa hukuncin mazaunin unguwar Bachirawa Quarters da ke karamar hukumar Dala a Kano ya kawo wata yarinya zuwa Kano ba bisa ka’ida ba.

“Idris ya kawo wata mai suna Mary David, ‘yar shekara 16, daga karamar hukumar Ise Orun ta Ekiti zuwa Kano ba bisa ka’ida ba a ranar 24 ga watan Janairu, domin ya yi mata hanyar balaguro zuwa Libya,” inji shi.

Ya kara da cewa laifin ya ci karo da dokar hana fataucin mutane ta shekarar 2015 kuma laifi ne da ake hukunta wanda aka samu dashi

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button