Ƴan wasan Kano Pillars sun yi haɗari a hanyar Jos


Tawagar kungiyar kwallon kafa ta ‘yan kasa da shekaru 19 na Kano Pillars ta yi haɗari.
Tawagar tayi haɗarin ne a hanyarsu ta zuwa filin wasa na Jos domin buga wasa a gasar matasa ta ‘yan kasa da shekaru 19.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da sashin yada labarai na kungiyar ya fitar a yau Talata.
“Muna bakincin sanar da cewa, motar da ke dauke da tawagar U-19 ta Kano Pillars FC ta yi hatsarin mota a yau, yayin da take kan hanyarta zuwa Sabon Filin Wasa na Jos don buga wasan cikon mako na 5 a gasar matasa ta U-19 da Plateau United .
“Wasu daga cikin ‘yan wasan da direban sun ji rauni a wannan mummunan al’amari, kuma an gaggauta kai su asibiti don samun kulawar likitoci. Alhamdulillahi, ba a samu asarar rai ba a wannan lokaci, kuma tawagar likitocin na ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki.”
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




