Labarai

Yadda direban mota ya katso bayan gidansa inda ya shafawa jami’in kula da titin da ya je kama shi

Advertisment

Wani bidiyo da yake yawo a yanar gizo ya bayyana yadda direban wata mota ya tube kayansa, yayi bayan gida a hannunsa sannan ya shafawa jami’in LASTMA wanda yayi yunkurin kama shi, LIB ta ruwaito LH na rahoto

Lamarin ya auku ne a Jihar Legas wanda ya janyo mutane su ka taru suna ganin ikon Allah.

Duk da dai ba a tabbatar da wanne bangare bane a cikin Jihar Legas, amma an ga yadda direban ya tube tsirara tare da tsugunnawa yana bayan gida a hannunsa.

 

Advertisment


Bayan kammala bayan gidan ne ya shafawa jami’in hukumar kula da dokokin titin Jihar Legas wanda cikin gaggawa ya sauka daga motar tasa.

Lamarin ya bai wa kowa mamaki akan yadda direban ya nuna rashin sanin darajar kansa don bai damu da tsiraicinsa ba.

Wasu kuma su na ganin jami’in zai iya daukar cuta sakamakon yadda direban ya shafa masa bayan gidan.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button