Tsoho mafi zaman cikin tashin hankali da ta taba gani ba (bidiyo)
Wannan dattijo Bai taba haihuwa ba, ‘yan uwansa yan bindiga duk sun kashe su.
Ya yi gudun hijira daga kauyensu zuwa Gusau inda yake kwana shi da Mai dakinsa ruwa sun cika dakin.
Wanda haka ya sa ya Kamu da rashin lafiyar da har mazakutarsa ta fashe da Marenansa. Bai taba zuwa assibiti ba Don bai da wanda zai Kai shi assibiti kullum cikin kuka yake.
Wanda yanzu haka suna kwana a inda ake dafuwar abinci (kitchen) duk zafi ko sanyi nan yake rayuwa. Mu taimaka don ceto rayuwar wannan bawan Allah, Musamman mu Kai shi assibiti don ceto rayuwaesa.
Ga bidiyon nan.
Ga Wanda ke son taimaka masa Kai tsaye zai iya zuwa unguwar Gwaza Gusau jihar Zamfara.
Ga Mai son taimakawa ko da Naira ce Don ganin an kai shi assibiti kai tsaye zai iya tura tallafinsa a wannan asusun Ajiya na banki Kamar haka:
Maibiredi Charity Foundation
2045281721
First Bank
Don Karin bayani a Kira
ko WhatsApp 👇
08069807496
Mu taimaka ko da addu’a ce ko share na wannan labari ko Allah ya sa a dace
Allah ya ba mu Ikon taimakawa