Labarai
Hisbah ta haramta caca da harkar mata masu zaman kansu a fadin jihar Katsina
Advertisment
Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta sanar da haramta duk wani nau’in caca da harkar mata masu zaman kansu wato sana’ar karuwanci a duk fadin jihar.
Bayanin hakan na cikin wani kunshin dokoki da hukumar ta fitar a Katsina daga ofishin babban Kwamandan hukumar Dr Aminu Usman Abu Ammar, inda ta ce ta kuma haramta masu sana’ar haya da babura wato “achaba” su rika daukar mata sama da daya ko goyon mace da namiji a kan baburansu.
Hukumar ta ce ta dauki wannan matakin ne bisa la’akari da lalacewar tarbiyya da ke neman ya yawaita a cikin al’umma.
Hukumar ta ja hankalin iyaye da su saka idanu sosai kan ‘ya’yansu, domin tarbiyya ta inganta a cikin al’umma.
Advertisment
Saurari cikakken bayyani