Wasu Mabiya Kungiyar Hakika, Sun Tabka Wa Matar Aure Ciki A Jihar Katsina


Matar ce ta fara nuna wa matasan uku cewa tana bukatar shiga kungiyar kafin su yi mata ciki. Fasikanci da matar na daya daga cikin Ka’idojin da Mabiya Kungiyar ta Hakika suka fada mata kafin ta shiga kungiyar. Mijin matar ya ce yayi tafiya zuwa Legas inda ya kwashe shekara daya, da ya dawo sai ya ga matarshi da jaririn wata hudu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta cafke wasu matasa uku, mabiya kungiyar Hakika, bisa zargin jan ra’ayin wata matar aure mai suna Zainab Ahmed, inda su kai mata ciki, bisa cewar za su sanya ta cikin tafiyar kungiyar ta harkar.
Wadanda ake zargin su ne, Tukur Dan-Azumi, mai shekara 19, Abubakar Yahuza mai shekara 20, sai Kuma Rufa’i Saosi, mai shekar 27, wadanda dukkanin su, mazauna kauyen Unguwar Dantalle na yankin Tandama da ke karamar hukumar Danja ne.
Rahotanni sun nuna cewa Zainab Ahmed, ta bayyana cewa, “Na sheda masu cewa, ina son in shiga cikin kungiyar ta Hakika, inda suka sheda min cewa, akwai ka’ida daya da zan bin, kafin in shiga harkar, wacce ita ce sai sun sadu dani.” inji ta.
A cikin sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta fitar, ta bayyana cewa, “Mijin matar mai suna Isiyaku ne, ya kai wa rundunar ‘yan sandan rahoton faruwar lamarin, inda bayan ya dawo daga jihar Legas, inda ya kwashe shekara daya a can, bayan iso gida kuwa, shine ya iske matarsa da jaririya Mai kimanin wata hudu da haihuwa” inji sanarwar
Zuma times hausa na wallafa wannan labari