Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya

An katse babban layin wutar lantarkin ne da misalin ƙarfe 2.19 na safe, ranar 3 ga watan Yunin 2024,” in ji sanarwar da kakakin kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya fitar ranar Litinin.

Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya
Babban layin wutar lantarki

Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta katse babban layin wutar lantarki na Nijeriya
Ƙungiyar Ƙwadago ta NLC ta katse
babban layin wutar lantarki na Nijeriya lamarin da ya jefa dukkan ƙasar cikin duhu, a cewar kamfanin da ke rarraba hasken lantarki na ƙasar (TCN).

“An katse babban layin wutar lantarkin ne da misalin ƙarfe 2.19 na safe, ranar 3 ga watan Yunin 2024,” in ji sanarwar da kakakin kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya fitar ranar Litinin.

Hakan na faruwa ne a yayin da gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago ta NLC da TUC a Nijeriya ta sha alwashin tsunduma yajin aiki tare da kassarar harkokin ƙasar domin tursasa wa gwamnatin Bola Tinubu ta riƙa biyan ma’aikata aƙalla N497,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Ganawar da shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar wakilai Tajedeed Abbas suka yi da wakilan ‘yan ƙwadagon ranar Lahadi ta gaza shawo kan yunƙurin shiga yajin aikin.

TRT AFRIKA HAUSA

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button