Labarai

Lauyan Abduljabbar ya nemi a biya shi Naira Miliyan ₦20 saboda ɓata masa Lokaci da an kayi

Babbar kotun jaha a ɓangaren ɗaukaka ƙara ƙarƙashin masu Shari’a Aisha Mahamud, da Nasir Saminu, sun sanya ranar 9 ga wannan watan da ake ciki dan ci gaba da sauraron daukaka karar, da Abduljabbar Nasir Kabara ya shigar.

A zaman kotun na yau lauyan Abduljabbar, Barrista Yusuf Sadik, ya shaidawa kotun cewar a shirye suke a fara sauraron daukaka karar.

Sai dai lauyan gwamnati ya bayyana cewar basu shirya ba dan haka a sanya wata ranar.

Majiyarmu ta samu wannan labari daga Dala Fm kano,Lauyan Abduljabbar ya shaidawa kotun cewar sun bai wa lauyoyin gwamnati takardun bayaninsu tun a watan 2 da ya gabata, dan haka a biya Abduljabbarun Naira miliyan 20 saboda ɓata masa lokaci da aka yi.

Sai dai lauyan gwamnati ya yi suka an kuma duba lokacin da aka bada takardun a watan uku ne dan haka wannan lauya ya janye rokonsa.

Daga nan ne kotun ta sanya ranar 9 ga watan nan na Mayu da ake ciki, an kuma umarci lauyan gwamnati da ya yi martani idan yana da shi kafin wannnan rana.

Wakilinmu na Kotu Yusuf Nadabo Isma’il ya rawaito cewa, Abduljabbar Nasir Kabara dai ya daukaka karar ne dan kalubalantar hukuncin kutun shari’ar muslunci ta kofar kudu, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanya rataya bisa samunsa da laifin ɓatanci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button