Labarai

Na biya G-fresh Al’ameen maƙudan kudi ya sake ni, Babu aure ni da shi – Sadiya Haruna

Advertisment

Idan baku manta an dade ana dambarwa aure tsakanin Al’ameen G-fresh da sayyada sadiya haruna wanda har abun yaje har gaban kotu wanda anka nemi sasancin tsakanin ma’aurata biyu.

To a yau shine gidan rediyo freedom sun samu zantawa da ita amarya sayyada sadiya haruna akan makomar aurensu yake domin har yanzu, shi angon Al’ameen G-fresh yana iƙirarin matarsa ce.

Freedom Radio ta yi ƙoƙarin jin ta bakin G-Fresh sai dai har kawo lokacin haɗa wannan rahoto ba mu same shi ba.

Ga abinda take cewa a cikin wani sautin murya.

Ana rade raden Shari’arku da G-fresh yazo karshe minene ya faru ?

“Eh Shari’a yazo ashe malam garba akan dubu ɗari biyar ne ₦500,000 ne yake wahalda Shari’ah kullum yace yana son matarshi yaki fito mana a mutum amma Alhamdullahi wanann karo ya fito a mutum matsalar sa dai dubu ɗari biyar ne na bashi, kamar yadda ya furta a baki ya ƙara rubuta takarda a rubuce bani ba shi har abada.

Ina masa fatan alkhairi Allah ya hada kowa da dai-dai sa.

Yanzu kenan za’a ce ba kare bin damo ba maganar biko?

Haba kai ko auren da anka shafe wata takwas ba’a tare , ba’a taɓayin kwana daya na farin ciki ba, ina zancen biko a wannan lamari kamar dai yadda na gayamaka Allah ya hada kowa da rabonsa, Allah ya hada kowa da dai-dainsa na masa fatan alkhairi.-inji sadiya haruna.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button