El-Rufai Ya Shirya Yin Fada da Gwamnatin Shugaba Tinubu


Watanni takwas bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da shi, rahotanni sun ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, zai fara taƙaddama da gwamnatin Bola Tinubu Duk da cewa suna jam’iyya ɗaya, akwai alamun cewa El-Rufai da Shugaba Tinubu ba aminan juna ba ne Bayan da aka hana shi damar zama minista a 2023, haɗe da jita-jitar da ake yaɗawa na cewa yana sha’awar shugabancin Najeriya a 2027,
El-Rufai ya yanke shawarar ɗaukar mataki
Nasir Ahmad El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna yana shirin “yaƙi” da Shugaba Bola Tinubu a aƙalla kotuna biyu. Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu, za a gabatar da faɗan ne a kotunan Najeriya.
El-Rufai na sa ran wanke sunansa daga zargin cewa yana da hatsarin tsaro wanda ya hana shi samun muƙamin minista.
Meyasa El-Rufai zai je kotu?
Tsohon gwamnan yana son wanke kansa ne bayan da wasu masu sharhi suka ce zai ƙalubalanci sake tsayawa takarar Shugaba Tinubu a 2027.
Rahotanni sun ce na kusa da El Rufa’i sun bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta wulaƙanta tsohon gwamnan a bainar jama’a.
Rashin samun muƙamin na El-Rufai ya ba na kusa da shi mamaki duba da irin rawar da ya taka wajen sanya gwamnonin Arewacin Najeriya suka marawa Tinubu baya a lokacin zaɓen 2023.
Jaridar Vanguard ta ambato wani na kusa da El Rufai yana cewa: “Kuna tunanin cewa Mallam zai bari wannan tambarin ya tsaya a kansa? Ina mai tabbatar muku da cewa zai wanke sunansa a gaban kotu.”
– Liberty Tv
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




