Me gwamnati ke yi da kuɗaɗen tallafi da ta cire


A jawabinsa na farko bayan shan rantsuwar kama mulki, ranar 29 ga watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye “tallafin mai”.
Shugaban ya ce matakin cire tallafin man fetur ɗin ya zama dole.
Mahukunta a ƙasar na kukan cewa tallafin man da gwamnati ke biya yana janye ɗumbin dukiyar da ya kamata a yi amfani da ita wajen samar da muhimman ababen more rayuwa.
Tun daga wannan furuci da ya yi aka shiga ruɗu, aka yi ta samun dogon layukan motoci a gidajen mai, kuɗin sufuri ya tashi, inda gidajen mai ɗin suka koma sayar da litar mai kan naira 700.
Bayan haka ne kuma, ƙungiyar kwadago a ƙasar ta tsunduma yajin aikin gargaɗi domin nuna adawa da matakin da gwamnatin ta ɗauka na cire tallafin.
Ƙungiyar ta ce babu abin da cire tallafin ya yi illa ƙarin wahalhalu ga ƴan Najeriya.
Ba ya ga tallafin man fetur, akwai kuma batun cire tallafin lantarki, inda tun a tsakiyar watan Fabrairu ne, ministan lantarki na Najeria, Adebayo Adelabu ya sanar da cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a kan wutar lantarki ba saboda tarin basukan da kamfanonin samar da lantarki ke bin gwamnati.
Sanarwar ta Adelabu ta janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta kasancewar ba a fita cikin kuncin da cire tallafin mai ya yi ba, sai ga na wutar lantarki.
Cire tallafi ya sa ana biyan albashi yadda ya kamata’
Gwamnatin shugaba Bola Tinubu dai ta ce za ta yi amfani da kuɗaɗen tallafin da ta cire wajen yi wa ƴan ƙasar ayyukan more rayuwa kamar hanyoyi da sauransu.
Mai magana da yawun shugaban Najeriyar Abdul’aziz Abdul’aziz ya faɗa wa BBC cewa ba wai gwamnati ta ware kuɗin ne tana ajiye su a wani asusu ba kamar yadda wasu ke bayyanawa.
“Kuɗin tallafi ba kuɗi ne na daban da aka ware su ba. Dalilin cire tallafi shi ne saboda an samu ƙarin kuɗin shiga wanda ya sa yanzu ana biyan albashi. Idan da ba a cire shi ba da jihohi ba za su samu damar biyan albashi ba,” in ji shi.
Ya ce yanzu jihohi na samun damar biyan albashi yadda ya kamata saboda cire tallafi, ana kuma yin ayyuka duka a matakin gwamnatin tarayya da kuma na jihohi.
Kakakin shugaban Najeriyar ya ce cikin abubuwan da ake yi bayan cire tallafi shi ne fara rabon kuɗaɗen taimako da na bashi da ya kai kusan naira biliyan 200.
“Akwai kuma manyan ayyuka na titi da jirgin ƙasa waɗanda ake yi sakamakon ƙarin kuɗaɗen. Duk gwamnoni da ke aiki a jihohinsu suna yi saboda samun ƙarin kuɗin cire tallafi,” in ji shi.
Ya ce a baya ana yawan samun ƙorafi kan rashin biyan albashi a jihohi da kuma ƙananan hukumomi, amma yanzu babu duka wannan.
Abdul’aziz ya kuma musanta rahotanni da ke cewa gwamnati na biyan kuɗin tallafi fiye da a baya, inda ya ce da akwai haka da batun ba zai ɓuya ba.
“Ba za a ɗauki kuɗi kuma ana samun ƙarin kuɗin shiga, sannan a ce ana biyan tallafin mai ba,” a cewar kakakin shugaban Najeriyar.