Fadar Sarkin Musulmin Najeriya ta ce Talata za a fara duba watan Shawwal
Fadar Sarkin Musulmin Najeriya ta ce Talata za a fara duba watan Shawwal
Kwamitin ganin wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar su fara dibon watan Shawwal a ranar Talata
Kamar yadda bbchausa na ruwaito.Sanarwar da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce Talata ta kama 29 ga watan Ramadan daidai da 11 ga watan Mayu.
Majalisar Ƙoli ta Musulmi a Najeriya, NSCIA ta ce idan har Allah ya sa an ga watan, Sarkin Musulmi zai bayar da sanarwar ayyana Laraba a matsayin 1 ga watan Shawwal.
“Amma idan ba a ga wata ba ranar Talata, to kai tsaye Alhamis za ta kasance ranar Sallah a matsayin 1 ga Shawwal,” in ji sanarwar da NSCIA ta fitar a Twitter.
If, however, the crescent is not sighted on Tuesday night, Thursday, 13th May, 2021 automatically becomes the first of Shawwal, 1442 AH (‘Id day). A press statement to that effect would be issued on Tuesday night.
— NSCIA — Islamic Affairs (@NSCIAng) May 8, 2021
Bisa al’ada idan an ga watan ana sanar da Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.