Shin da gaske Murja kunya tayi Aure?
Labarin cikin wani faifan bidiyo da ake yadawa cewa murja Ibrahim kunya tayi aure wanda abun ya jawo cece kuce.
Wanda shine jaridar Dclhausa ta samu tattaunawa da lauyan murja kunya akan maganar shin da gaske murya kunya tayi aure wanda a cikin sharuddan bada belin ta yana daga cikin haramta amfani da kafar sada zumunta.
Ga abin da lauya yake fadi.
Shi alamarin aure abu ne mai kyau kuma abin farin ciki Sosai in kuma ya afku za’a so hakan amma ilimi da tunani na banda masaniya anyi auren nan, amma nasan akwai kishin kishin cewa akwai mane mi kuma iyaye sun sani da sauran su, wanda nima na hadu da shi na ganshi, kuma na samu labari ta ɓangagorin su shi mai nema da wadda ake nema.
Amma ban sani ba idan har al’amarin ya tabbata wanda ake magana kuma idan har ya tabbata nima zan so hakan da shi ne , ko ko da wani ne bansani ba.
Yanzu ina magana ne na matsayina Au hajji banda masaniya auren nan anyi.
A matsayin ka na lauyanta yaushe rabonka da haduwa da ita.?
Eh tun ranar da munka fito daga kotu , tun da dai yanzu harka ce ta waya kila yakan shafe haduwa din, amma gaskiya koda ya faru banda masaniya, amma zanyi mamaki idan har naji tunda macece wadda a sananiya.
Yana da kyau ace kana da masaniya a matsayin ka na lauyanta?
Ba dole duk motsi nata ba , tana da rayuwar ta a matsayin murja, kuma tana da rayuwa a matsayin murja client su Au hajji, to saboda haka rayuwar ta ta murja Ibrahim daban, rayuwarta ta murja Ibrahim client au hajji to wannan muna da cikakken sanin duk wani motsin ta, amma rayuwa ta ta daban wannan bamu da masaniya akan ta.
Zaku iya sauraren karin bayyani a nan.