Labarai

Buhari Ya Fadi Hanya 1 da ‘Yan Najeriya Za Su Samu Sauki

Advertisment

Yayin da ake ci gaba da bukukuwan salla karama, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya al’ummar Musulmai murna Buhari ya bayyana cewa hadin kai da goyon baya ga shugabanni ne kadai zai kawo ci gaba a kasar musamman a wannan yanayi Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon shugaban ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba 10 ga watan Afrilu

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya al’ummar Musulmai murnan sallar azumi. Buhari ya shawarci ‘yan kasar da su goyawa shugabanni baya domin samun ci gaba a kasar.

Wace shawara Buhari ya ba ‘yan Najeriya?

Ya ce goyon bayan shugabanni ne kadai zai inganta kasar musamman a wannan yanayi da ake ciki.
“Goyon bayan shugabanni da hadin kai a Najeriya shi ne zai kara inganta kasar.” “Ya na da matukar muhimmanci a hada kai domin kare martabar Najeriya da kuma inganta ts.” – Muhammadu Buhari Buhari ya yi godiya.

-Liberty tv

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button