Kannywood

Daddy hikima abale yayi magana ta hikima akan halin da Adam a zango yake ciki

Advertisment

Shahararren jarumi nan daddy hikima abale wanda anka fi sani da abale yayi dan gajeren bidiyon akan halin da abokin aikinsa yake ciki wato adam a zango akan irin magananu da yake sake a kafaffen sada zumunta wanda abubuwan idan kaji zaka tausawa jarumin.

Adam a zango abun na ci masa tuwo a kwarya a duk lokacin da ake jifarsa da kalma auri saki.

A nan shawara biyu ce daddy hikima abale yake baiwa ta farko adam a zango da kuma ita kanta masana’atar Kannywood.

“A gurguje zanyi magana akan adam a zango abubuwa ne guda biyu ta farko shi halin da yake ciki da kuma mu yan masana’atar Kannywood, akan yan masana’atar Kannywood irin wanann abubuwan da yake fadi daga cikin mu a kira shi a ja shi a jiki aji micece matsalar taya za’a taimake shi, wasu har dariya suke masa kaza ya samu kaza yaci kaza duk wannan abubuwa ne da bai dace ba.

Saboda halin da adamu yake ciki a yanzu ko yau ko gobe kowa zai iya tsintar kansa a wannan yanayin saboda inda kai jarumi ne, darakta ko furodusa dole zaka iya tsintar kanka a wannan halin, to abinda ya kamata a jashi a ciki aji minene matsalar sa ta ina za’a taimake sa, haka shima sai aji shawarwarin da za’a bashi ko minene tsanani akwai sauki a cikinsa.

Da farko Adamu karka manta duk abinda yayi tsanani karka manta Allah , Allah shi yake yi, ba mai bayar da shiriya ko rahama sai Allah ya kamata a nuna masa ga yadda rayuwa take ciki dukkan rayuwar da ka tsinci kanka a ciki da addu’o’i da manzon Allah (s.a.w) ya koya mana ko damuwa kakeji kayi sallati Allah zai sanyaya sauki a zuciyarka.”inji daddy hikima abale.

Ta yaya muke rayuwa a kannywood?

 

Yan kannywood 60% muna rayuwa ba dan Allah ba, idan zanyi rayuwa da wane minene zan samu to kuma wannan ba rayuwa ba ce ta addini ba ya kamata mu gyara wannan matsalolin mu, yau wane ya tafi gobe wane ya tafi gobe kai ne, gobe nine ba wanda ya sani to ko minene rayuwa kada ka manta Allah, allah ya datar damu Allah yasa mudace.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button